kasashe 26 ne ke aikin neman jirgin Malaysia da ya bace

Kwanaki bayan bacewar jirgin saman Malaysia mai dauke da fasinjoji 239 kawo yanzu kasashe 26 ne ke ci gaba da aikin neman jirgin amma ba amo ba labari. A cewar Ministan Sufurin Malaysia binciken gano jirgin abu ne gagarumi da ya sha karfin kasa daya saboda ba wanda ke da tabbacin inda jirgin ya bace. […]

kasashe 26 ne ke aikin neman jirgin Malaysia da ya bace
kasashe 26 ne ke aikin neman jirgin Malaysia da ya bace

Kwanaki bayan bacewar jirgin saman Malaysia mai dauke da fasinjoji 239 kawo yanzu kasashe 26 ne ke ci gaba da aikin neman jirgin amma ba amo ba labari.
A cewar Ministan Sufurin Malaysia binciken gano jirgin abu ne gagarumi da ya sha karfin kasa daya saboda ba wanda ke da tabbacin inda jirgin ya bace. Ya kara da cewa binciken ya shafi yankin kasashe da dama shi ya sa aikin ke bukatar  gayyar kasashe.
Jirgin mai suna Boeing 777 ya bace ne a safiyar 8 ga watan Maris bayan ya kama hanyar zuwa birnin Beijing daga garin Kuala Lumpur, babban birnin kasar Malaysia. Hukumomi a Malaysia dai sun ce sun yi amannar cewa da gangan aka karkata akalar jirgin amma ba su da masaniya kan dalilin yin hakan.
‘Yan sandan kasar Maldibes  dai sun ce  suna binciken wani rahoto da ke cewa a ranar da lamarin ya faru, wasu mutane sun ga wani jirgi da yake kokarin sauka kusa da tsibirin da suke zaune. Hukumoni  Malaysia sun yi maraba da wannan bayanin kuma sun bukaci karin bayanai daga jama’a wadanda za su taimaka don ganin an gano jirgin .
‘Yan uwan wadanda ke cikin jirgin na ci gaba da bayyana damuwarsu , a daya bangaran kuma hukumoni na ba da tabbacin cewa aikin neman jirgin zai kai ga samun nasara.