Kasashe 5 da mata ke auren namiji fiye da daya a lokaci guda
A al’adance namiji ne ke auren mace fiye da guda daya.
Bisa ga al’ada da addini, idan aka yi magana kan namiji ya auri mace fiye da daya, wannan ba sabon abu ba ne.
Al’adu da addinai da yawa sun yi tarayya kan mace ta auri namiji daya tak ne, yayin da namiji ke iya auren mace fiye da daya.
- Mutum Miliyan 1 ne Ke bukatar Tallafi a Arewa Maso Gabas —Ministar Jinkai
- Rasha ta dauki alhakin harin jirgin kasan Ukraine da ya kashe mutane da dama
Wannan al’ada an samu kasashe da dama sun yarda mace ta auri namiji daya ne.
Sai dai wasu kasashe sun sha bamban a wannan batu, inda mata suke auren namiji fiye da daya kuma a lokaci guda.
Wadannan kasashe su ne:
Indiya: Kabilar Kinnaur da Himachal da ke Paharis a yankin Jaunsarbawar a Arewacin Indiya da wasu tsirarun kabilu mace na auren namiji fiye da daya a lokaci guda.
China: A kasar China ma akwai wasu kabilu kamar Tamang da Kiang da Sherpa da Lhoba da ke yankin Tibet da mace ke auren namiji fiye da guda daya a lokaci guda.
Kenya: A Kenya ma mace na iya auren miji sama da daya, duk da dai cewa ana ce-ce-ku-ce a kan lamarin, amma gwamnatin kasar ba ta haramta hakan ba.
An taba samun wata mata daga kabilar Massai da ta taba auren maza biyu da take kauna a 2013.
Gabon: A Gabon ma dai kusan haka tsarin yake, mace na da ikon auren miji fiye da daya.
A al’adance namiji ne ke auren mace fiye da guda daya, amma a shekarar 2021 an taba samun wata mata da ta bayyana yadda ta auri maza bakwai kuma take zaune da kowane ba tare da wata matsala a tsakaninsu ba.
Nepal:
A Kudancin Nepal akwai kabilun Humla da Kosi da Dolpa da ke yin irin wannan aure, inda mace ke iya auren namiji fiye da daya. Amma duk da dokar da gwamnatin kasar ta yi a 1963 na hana hakan, sun ci gaba da yin wannan aure.