Kasashen da ka iya kai labari a Gasar Euro bana
Masana harkar kwallon kafa sun yi hasashen kasar da za ta lashe Gasar Euro
Ranar Asabar aka fara fafatawa a zagaye na biyu na Gasar Euro ta bana, inda Italiya ta doke Austria da ci biyu da daya sannan Denmark ta doke Wales, kasarsu Gareth Bale. da ci hudu da nema.
A shafinmu na ‘Bakin Raga’, fitattun masu sharhi a kan wasanni, Mubarak Abubakar da Salisu Musa Jegus da Isiyaku Muhammaed, sun tattauna, inda suka warware zare da abawa a kan kasashen da za ka iya lashe gasar ta bana.
- Tsohon Zakaran Duniya A Tseren Gudu Ya Mutu
- ’Yan Wasa 20 Da Ke Sahun Gaba Wajen Lashe Kyautar Balon D’Or A Bana
A cewar Salisu Jegus, “A ganina da ra’ayina, Ingila da Belgium da Italiya da Faransa ne za su iya lashe gasar Euro ta bana,” sannan ya kara da cewa Faransa ce ta fi sauran karfi, saboda haka yake tunanin ita ce za ta iya lashe gasar.
A nasa bangaren, Mubarak Abubakar cewa ya yi, “Italiya da Belgium da Denmark na cikin kasashen da nake ganin za su cinye,” sannan ya kara da cewa kasar Italiya ce ke kan gaba, hakan kuma ya sa yake tunanin ita za ta lashe gasar.
Da Isiyaku Muhammaed ya tambaye su dalilan zabinsu, sai Mubarak ya ce, “Ita dai gasa irin wannan wacce ake kira tournament [wadda ba ta] fi wasanni takwas ba gaba daya, akasari za ka samu kasashe masu ‘yan wasan da suka goge (experience) su ne suka fi lashewa.
Faransa ko Italiya
“Abu na biyu, akwai ‘yan baya gogaggu wadanda za su taimaka wajen hana shigar kwallaye, musamman irin wadanda bai kamata a yi sakaci su shiga ba.
“Sannan akwai gola wanda a karan kansa jagora ne kuma jarumi.
“[Abu] na uku, tsakiyar fili da suke da motsi kuma suke iya kwantar da hankalin wasa, wadanda suka kware a dauki zura, abin da Bature ke kira da counter attack.”
A nasa bangaren, Salisu Musa Jegus cewa ya yi a game da kasar Faransa, “Na farko har yanzu akwai karsashin nasarar da suka samu a wasan Gasar Kwallon Kafa ta Duniya a Rasha.
“Na biyu, yadda ‘yan wasan kungiyar ke taka rawa a kungiyoyin su da yadda suka fara ita wannan gasar.
“Sai zaratan ‘yan gaba da kasar Faransa ke da su kamar su Mbape da Greizman; ga kuma karin karfi na dawowar Kareem Benzema bayan shekaru biyar ya sanya kungiyar Faransa samun karfi a gaba.”
Ya kara da cewa, “Tsakiyarsu kuwa da ma ba a magana – Pogba, Kante da sauransu suna da karfin basirar sauya fasalin wasa a ko wanne lokaci.”
Sai dai Isiyaku ya fada wa Jegus cewa a wasan Faransa da Portugal, ‘yan wasan tsakiya na Portugal, Sanchez da Danilo, ba su yi fice ba kamar na Faransa, amma a wasan sai suka ‘boye’ na Faransa.
Tasirin Ronaldo
Sai Jegus ya ce, “Wasa da Portugal a wannan gasar na da hadari saboda su ke rike da kofin, wannan kwarjinin yana da tasiri a wajen wasan kwallon kafa.
Bayan irin zaratan matasan ‘yan kwallo da suke da su, sannan duk lokacin da tawaga take da jagoran da yake da karfi da tasiri a duniyar wasan kwallon kafa to wasa da su sai an yi taka tsantsan.
“Tasirn Christiano Ronaldo a cikin wasa yana iya daukar kaso 49 cikin 100 na wasa tsakanin abokan karawarsu.”
A game da maganar Isiyaku cewa ‘yan wasan gaban Faransa ba sa zura kwallaye a gasar ta bana, sai Jegus ya ce, “Ba lallai sa ‘yan wasan gaba sun zura kwallo a raga tawaga take cika ba, wani abu da yake sanyawa ta bunkasa tare da samun nasara shi ne tsarinta da fahimtar ‘yan wasa a tsakaninsu da kuma cikakkiyar fahimta da yarda a tsakaninsu da mai horar da su sai kuma uwa-uba magoya baya.
“Sannan salon yadda suke buga wasa zai iya bai wa kowa damar ya sanya kwallo a raga kuma da ma kungiya idan ta isa shi ne kowa na iya sanya kwallo a zare ba tare da dogaro da wani dan wasa daya ba.”
Denmark fa?
Shi kuma Mubarak cewa ya yi a game ta Italiya, “Ta kafa sabon tarihi na yin wasa 31 ba tare da ta yi rashin nasara ba,” sannan ya kara da cewa kasa ta biyu da yake tunanin za ta iya ba da mamaki ita ce kasar Denmark, wadda a game da ita ya ce, “duba da yadda suke kai hare-hare a wasanninsu ba kakkautawa, da kuma tarihin da suka kafa na kasa ta farko a tarihin wannan gasa da suka jefa kwallo hudu ko sama da haka a wasa biyu a jere, za su iya lashe wannan gasa in har suka ci gaba da tafiya a haka.”
Sannan a game da kasar Faransa da Jegus ya ce za ta iya lashe gasar, Mubarak cewa ya yi, “Duk da Faransa ana mata kallon ta fi kowa damar cinye wannan gasa, ba na jin za su tsallake matakin kusa da na karshe.”
Ko ma dai yaya za ta kasance, za mu sake dawowa domin tattunawa a kan wannan batu bayan wasan karshe.
Amma kafin nan za ku iya ci gaba da muhawara a shafukanmu na sada zumunta. Ku latsa hoton da ke kasa ku fadi ra;ayinku.