Kasashen da suka rage a Gasar Kofin Duniya ta ’yan kasa da shekaru 20
Koriya ta Kudu ta fatattako tawagar Flying Eagles ta Najeriya.
Yanzu haka ana ci gaba da fafatawa a Gasar Kofin Duniya ta ’yan kasa da shekara 20 wadda kasar Argentina ta kasance mai masaukin baki.
Koriya ta Kudu da Uruguay sun kai zagayen kusa da na karshe a gasar wadda Hukumar Kwallon Kafa ta Duniya FIFA ke jagoranta.
- Yemi Mobolade: Dan Najeriya ya zama Magajin Gari a Amurka
- Cire Tallafin Mai: An rage ranakun zuwa aiki zuwa kwana 3 a Kwara
Uruguay ta doke Amurka da ci 2-0 a Santiago del Estero, inda suka mamaye wasan daga farko har karshe kamar yadda Kamfanin Dillancin Labarai na AP ya ruwaito.
Ita kuwa Koriya Ta Kudu ta doke Najeriya ne da ci 1-0 bayan da aka kara lokaci.
Yanzu Uruguay za ta fafata da Isra’ila a ranar Alhamis yayin da Koriya ta Kudu kuma za ta gwada kwanjinta da Italiya don neman gurbi a wasan karshe.
Gasar ta bana wadda aka soma tun a ranar 20 ga watan Mayun da ya gabata ita ce karo na 23 da Hukumar FIFA ta shirya a tarihi.