Kasashen da suke azumi mafi tsawo ko gajarta a duniya
Me ya sa ake fara Ramadan a lokuta daban-daban?
Me ya sa ake fara Ramadan a lokuta daban-daban? Akan samun raguwar kwana 10 zuwa 11 a kowace shekara idan aka kwatanta da lokacin da aka fara azumin a shekarar da ta gabata.
Hakan ya samo asali ne kan yadda watannin Musulunci ke da kwanaki 29 zuwa 30.
- Goman karshe: Dama ta karshe ga mai neman rahamar Allah
- Wa’azi: Gwamnatin Bauchi ta gargadi malamai kan tada zaune-tsaye
A shekarar Miladiyya kuma akwai mai kwana 28 kamar Fabrairu da kuma masu kwana 31.
Saboda kwanakin shekarar Hijira sun gaza na Miladiyya da kwana 11, hakan ya sa za a yi azumin watan Ramadan sau biyu a shekarar 2030 — a fara na farko ran 5 ga Janairu na biyu ranar 25 ga Disamba.
Kasashen da suke yin azumi mafi gajarta a 2023
A bana Musulmin da ke kasar Chile suna yin azumi mafi gajarta na tsawon sa’a 11 da rabi a kullum.
Sai su New Zealand da Ajentina da Afirka ta Kudu, suna yin azumin sa’a 11 zuwa 12.
Kasashen da suke yin azumi mafi tsawo a bana
Musulmin birnin Reykjabík da ke Iceland, azuminsu zai zama cikin mafi tsawo a bana. Ana hasashen suna yin azumi sa’a 16 da minti 50 a kowace rana.
Najeriya: Sa’a 13 da minti 18 zuwa 13 da minti 25
Tunisiya: Awa 13 da minti 44, zuwa 14 da minti 55
Maroko: 13 da minti 37, zuwa 14 da minti 41
Masar: mara tsayi — Awa 13 da minti 39, zuwa 14 da minti 34
Saudiyya: Awa 13 da minti 29 zuwa 14 da minti 11
Katar: Awa 13 da minti 29 zuwa 14 da minti 13
Somaliya: Awa 13 da minti 22 zuwa 13 da minti 27.