kasashen duniya sun yi tur da kisan gillar masu zanga-zanga a Masar

kasashen duniya, wadanda suka had ada katar da Turkiyya sun yi suka da kakkausar murya kan irin kisan gillar da aka yi wa magoya bayan Muhammad Mursi a sansaninsu da ke Alkahira. Shi ma Babban Sakataren Majalisar dinkin Duniya ya yi Allah wadai da amfani da karfi da jami’an tsaron Masar suka yi don kawar […]

kasashen duniya sun yi tur da kisan gillar masu zanga-zanga a Masar

Magoya bayan Mursi a filin dagakasashen duniya, wadanda suka had ada katar da Turkiyya sun yi suka da kakkausar murya kan irin kisan gillar da aka yi wa magoya bayan Muhammad Mursi a sansaninsu da ke Alkahira. Shi ma Babban Sakataren Majalisar dinkin Duniya ya yi Allah wadai da amfani da karfi da jami’an tsaron Masar suka yi don kawar da masu zanga-zanmgha.
kasar katar, wadda ita kadai ce a kasashen Larabawa ke goyon bayan ’yan uwa Musulmi magoya bayan Muhammad Mursi ta fitar da sanarwar, inda suka yi tur da amfani da karfi da tursasawa a kan masu znga-zangar lumana, kamar yadda Kamfanin Dillancin Labaran kasar kNA ya ruwaito.
Turkiyyakuwa ta bukaci Hujkumar Tsaro ta Majalisar dinkin Duniya da kungiyar kasashen Larabawa su dauki matakin shawo kan kisan gillar da ake yi wa al’umma,” kamar yadda Firayiministan kasar ya bayyana.
Jami’ar Azhar ba ta goyon bayan harin da aka kai wa magoya bayan Mursi da ke zanga-zangar lumana. Babban Limamin Jami’ar Ahmed Al Tayyeb, ya yi nuni da cewa: “Bat a da masaniya kan wannan mataki da aka dauka na tarwatsa masu zanga-zanga, su m ta kafar yada labarai suka samu labara,”  a cewarsa, don haka ya yi tur da amfani da karfi, al’amarin da ya bayyana cewa ba zai yi maganin matsalar da ake fama da ita ba.
Tarayyar Turai ma ba ta goyin bayan matakin da gwamnatin rikon ke dauka ba, amma ana ganin tamkar Amurka na goyon bayan gwamnatin rikon, domin har yanzu ba tabbatar da cewa juyin mulki aka yi wa zababbiyar gwamnatin dimokuradiyya ta Masar, kamar yadda masu sharhi suka tabbatar.
Jami’an tsaron Masar sun bude wuta a kan masu zanga-zanga, a wani karon batta da aka yi tsakanin magoya bayan hambararren shugabn kasar, Muhammad Mursi da sojoji da ’yan sanda, inda kididdigar gwamnati ta nuna an salwantar da rayukan mutane 124.
Can kuwa a filin masallacin Rabaa al-Adawiya da ke Arewa maso Gabashin Alkahira, inda dubban magoya bayan Mursi suka yi zaman dirshan na tsawon makonni shida, ’yan sandan kwantar da tarzoma sun watsa musu barkonon tsohuwa, sannan suka kona tayuoyi, har hayaki ya balbale sararin samaniya.
A macuware adana gawa da kwe asibitin kusa da filin amsallacin. Wakilin Kamfanin Dillancin Labarai na Reuters ya kirga gawarwaki 29, wadanda suka hada da na karamin yaro dan shekara 12. Mafi yawan wadanda suka rasu, an kashe su ne a sanadiyyar harbin bindiga a ka. Wata malamar jinya a asibitin ta ce ta kirga gawarwaki 60, kuma ana sa ran yawan wadanda suka mutu su karu
Gwamnatin Masar ta kakabga dokar ta-baci a kasar, bayan da aka yi artabu da jami’an tsaro da magoya bayan hambararren shugaban kasa, Muhammad Mursi, inda aka yi wa dimbin mutane kisan gilla. Fadar Shugaban kasa ta bayar da sanarwar dokar ta-baci, wadda ta fara aiki daga karfe hudun ranar Larabar da ta gabata.
“Tsaro na fuskantar barazana saboda zagon kasa da hare-hare da ake kai wa kan gine-ginen gwamnati da na kamfanoni masu zaman kansu, ga yawan asarar rayukan masu ra’ayin Musulunci,” a cewar fadar shugaban kasa, don haka ta dauki wannan mataki.
Shugaban riko, adly Mansour ya bukaci sojojin su hada kai da ’yan sanda, su kuma dauki duk matakin da ya dace don tabbatar da tsaro, su kuma kare rayuka da dukiyoyin al’umma.”