kasashen Isra’ila da Falasdinu kowa na da hakkin mallakar kasarta – bin Salma

Yariman Saudiyya Mohammad bin Salman ya ce kasar Isra’ila da ta Falasdin suna da dama da hakkin mallakar kasarsu. kasar Saudiyya da ta Isra’ila ba su da wata alakar diflomasiyya mai karfi, amma a bayan fage yanzu an fara samun ci gaba a alakar da ke tsakanin kasashen biyu. Kwanan nan ne aka sanar da […]

kasashen Isra’ila da Falasdinu kowa na da hakkin mallakar kasarta – bin Salma

Yariman Saudiyya Mohammad bin Salman ya ce kasar Isra’ila da ta Falasdin suna da dama da hakkin mallakar kasarsu.

kasar Saudiyya da ta Isra’ila ba su da wata alakar diflomasiyya mai karfi, amma a bayan fage yanzu an fara samun ci gaba a alakar da ke tsakanin kasashen biyu.

Kwanan nan ne aka sanar da cewa kasar Saudiyya ta bayar da dama jirgi ya wuce ta sararin samaniyarta zuwa kasar Isra’ila, sai kuma kwatsam yanzu Yariman ya fitar da wannan jawabi cewa kasashen biyu suna da hakkin kasar, duk da cewa da yawa daga cikin kasashen Musulmi suna ganin cewa kasar ta Falasdinawa ce aka yi musu danniya da kwace.

An dade ana kai-komo game da hakkin mallakar yankin kasar Falasdinu, kuma an dade ana ba hammata iska.

Da yake amsa tambaya game da ko Yahudawa suna da hakkin mallakar yankin ‘asalin kasarsu’, sai ya ce, “Ina da yakinin cewa kowa, kuma a ko’ina, yana da hakkin zama lafiya. Ina da yakinin cewa da Falasdinawa da Yahudawa suna da hakkin mallakar kasarsu.”

“Amma kuma muna bukatar a samu yarjejeniya ta musamman da za ta tabbatar da zaman lafiya da kuma tabbatar da alaka da juna cikin mutunci,” inji shi.

Tun a shekarar 2002 kasar Saudiyya take kokarin samar da zaman lafiya  a tsakanin kasashen biyu a karkashin shirinta na Arab Peace Initiatibe.

Amma ba a taba samun wani babba daga kasar Saudiyya da ya taba amincewa kasar Isra’ila na da wani hakkin mallakar kasa ba.

Amma dai ya sanar da cewa akwai abin lura na addini a maganar, “Muna da matsala ta addini game da matsayin Masallacin kudus da ke birnin kudus da kuma matsayin Falasdinawa,” inji shi.