kasashen kungiyar kasuwanci ta duniya sun cin ma yarjejeniya kan kasuwanci
Wakilan kasashen da suka halarci taron kungiyar Kasuwanci Ta Duniya (WTO) da aka yi a Bali kasar Indonesiya sun cim ma yarjejeniya dangane da kasuwanci tsakanin kasashen kungiyar yadda kowace kasa za ta amfana. Wannan yarjejeniya ita ce irinta ta farko tun da aka kafa hukumar a shekarar 1995.Daraktan kungiyar kasuwanci ta duniya Roberto Azebedo wanda […]
PIC.14. A CROSS SECTION OF DIGNITARIES AT THE PRESENTATION OF THE 2014 FEDERAL BUDGET BY THE MINISTER OF FINANCE, DR NGOZI OKONJO-IWEALA IN ABUJA ON MONDAY (20/1/14). 385/20/1/14/CH/NAN

Wakilan kasashen da suka halarci taron kungiyar Kasuwanci Ta Duniya (WTO) da aka yi a Bali kasar Indonesiya sun cim ma yarjejeniya dangane da kasuwanci tsakanin kasashen kungiyar yadda kowace kasa za ta amfana.
Wannan yarjejeniya ita ce irinta ta farko tun da aka kafa hukumar a shekarar 1995.
Daraktan kungiyar kasuwanci ta duniya Roberto Azebedo wanda har sai da ya yi kwalla yayin bikin rufe taron. Ya ce a karon farko hukumar WTO ta yi abun da ya dace, wato ta haifi da mai ido.
Abu mafi mahimmanci da yarjejeniyar ta kunsa shi ne kawo sassauci dangane da ayyukan kwastan na kowace kasa yadda za su zama da adalci kuma a saukake ba tare da wata tangarda ba. Amma kafin dokar ta soma aiki sai gwamnatocin kasashe 159 da ke cikin kungiyar WTO sun amince.
Taron ya fuskanci barazana daga kasar Cuba wadda ta ce ba za ta amince da yarjejeniyar ba idan ba ta hada da cire mata takunkumin karya tattalin arziki da Amurka ta kakaba mata ba. Sai dai daga baya Cuban ta janye barazanar tata.
Masu nazari kan tattalin arziki sun kiyasta cewa yarjejeniyar za ta habbaka tattalin arzikin duniya da Dalar Amurka miliyan dubu daya ko tiriliyan daya a kowace shekara.