Kasashen Musulmi sun fusata kan kona Al-Qur’ani sau uku cikin wata daya
Magoya bayan jagoran mazhabar shi’a na Iraqi sun yi kira da a kona Ofishin Jakadancin Sweden.
Kona Al-Qur’ani sau uku a cikin wata daya a kasashen Denmark da Sweden ya jawo kakkausan suka, inda kasashen Musulmai suka bukaci a yi dokar da za ta hukunta masu yin wannan danyen-aikin a kasashen da ake kona littafin mai tsarki.
Jordan, Oman da Saudiyya sun yi gargadi game da yadda ake yawan kona Al-Qur’ani a Denmark, sannan suka bukaci birnin Copenhagen ya dauki matakai na hana ci gaba da aiwatar da irin wannan danyen aiki.
- Yadda ’yar shekara 3 ta zama miloniya daga zuwa sayen burodi
- Babu soyayya tsakanina da Hamisu Breaker – Momee Gombe
Ranar Asabar Jordan ta yi kakkausan suka bayan mambobin wata kungiya mai tsattauran ra’ayi sun kona A-Qur’ani a babban birnin Denmark, inda ta bayyana hakan a matsayin “kiyayya ga Musulunci.”
A wata sanarwa, Ma’aikatar Harkokin Wajen kasar ta yi Allah wadai da wannan aiki na rashin hankali wanda ke tunzura Musulmai da nuna kiyayya da kuma yin kafar-ungulu ga zaman lafiya.
Ta jaddada cewa kona Al-Qur’ani mai tsarki nuna kiyayya ce zalla ga Musulunci da rashin mutunci da rashin mutunta addini, sannan ta yi kira ga kasashen duniya su dauki mataki na hakika a kan batun.
Kazalika Ma’aikatar Harkokin Wajen ta yi kira a yi dokar da za ta hukunta masu yin wannan rashin hankali, sannan ta rika jaddada bukatar zaman lafiya da “amincewa da wadanda ba ku da ra’ayi iri daya” da hana tsattsauran ra’ayi.
Ita ma kasar Oman ta yi tir da kona littafin mai tsarki a babban birnin Denmark, tana mai bayyana hakan a matsayin yunkurin tunzura jama’a su tayar da rikici da kuma nuna kiyayya.
A wata sanarwa da ta fitar, Oman ta nemi kasashen duniya su “kalli irin wadannan matakai da ke cin fuska ga mabiya addinai da jefa kiyayya da gaba” a matsayin babban laifi.
Saudiyya ta magantu kan kona Al-Qur’ani
A wata sanarwa ta daban, Saudiyya ta yi Allah wadai da kona Al-Qur’ani a Denmark sannan ta nemi hukumomin kasar su dauki kwararan matakai na hana ci gaba da cin fuskar Musulmai.
Ma’aikatar Harkokin Wajen kasar ta fitar da sanarwa inda ta yi kassausan suka ga wannan mataki da ta bayyana a matsayin wanda ke tunzura mutane su yi rikici da kuma nuna kiyayya a tsakanin addinai.
Ta yi gargadin cewa sake yin wannan mummunan aiki zai sa Musulmai su kare kansu.
A ranar Juma’a ne mambobin wata kungiyar makiya Musulunci mai suna Danske Patrioter suka kona Al-Qur’ani mai tsarki a gaban Ofishin Jakadancin Iraki da ke birnin Copenhagen bayan ’yan sanda sun ba su kariya.
’Yan kungiyar sun ce sun dauki matakin ne domin mayar da martani ga harin da aka kai a ofishin jakadancin Sweden da ke birnin Bagadaza.
Ranar Alhamis da sassafe, dandazon masu zanga-zanga a Iraki sun cinna wuta a Ofishin Jakadancin Sweden da ke Bagadaza, don nuna fushinsu ga kona Al-Qur’ani da wani mutum mai suna Salwan Momika ya yi a Sweden ranar 28 ga watan Yuni daidai lokacin da ake bukukuwan Sallar Layya.
Wannan aika-aikar ce dai ta haifar da zanga-zanga da dama a kasashen musulmi kamar yadda gwamnatoci a Iraki, Turkiyya, Hadaddiyar Daular Larabawa, Jordan da Morocco suka yi tir da lamarin.
Dole masu wulakanta Al-Qur’ani su fuskanci hukunci mai tsauri — Khamenei
A jiya Asabar ce jagoran addini na kasar Iran, Ayatullah Ali Khamenei ya bayyana cewa ya zama wajibi mutanen da suka wulakanta Al-Qur’ani mai tsarki su fuskanci hukunci mai tsanani.
Ya kuma bukaci kasar Sweden da ta mika wadannan mutanen domin yi musu shari’a a kasashen musulmi, kamar yadda kafar yada labaran Iran ta ruwaito.
“Dukkan malaman Musulunci sun yi ittifaki kan cewa wadanda suka wulakanta Al-Qur’ani sun cancanci hukunci mafi tsauri.
“Hakkin da ke kan wannan gwamnatin ta Sweden shi ne mika masu laifi zuwa ga kasashen musulmi,” in ji Khamenei.
Iraki ta kori Jakadan Sweden
A bayan nan ne Iraki ta kori jakadan Sweden jim kadan bayan da masu zanga-zangar suka mamaye ofishin jakadancinta da ke Bagadaza tare da cinnawa wasu sassan ginin wuta.
Magoya bayan jagoran mazhabar shi’a na Iraqi Muqtada al-Sadr sun yi kira da a kona ofishin jakadancin Sweden din a ranar Alhamis.
Masu zanga-zangar dai sun fusata ne kan abin da ya ce shi ne karo na biyu da aka kona Qur’ani a gaban Ofishin Jakadancin Iraki da ke Stockholm.
A yayin da masu zanga-zanga a kasar Sweden suka yi ta harbi da kuma lalata wani littafi da suka ce Qur’ani ne, sai dai ba su kona shi ba kamar yadda suka yi barazanar yi.