…kasashen Musulmi sun kuduri aniyar taimaka wa Musulmin Myammar

kasashen da suka bai wa Musulmin Myammar agaji sun hada da Turkiyya da Bangladesh da Saudiyya, yayin da sauran takwarorinsu suka yi alkawarin ci gaba da kai agaji ga ’yan kabilar Rohingya da ake azabtar da su. kasashen Pakistan da Malesiya da Indonesiya su ne kan gaba wajen ganin an dauki matakin difulomasiya don shawo […]

…kasashen Musulmi sun kuduri aniyar taimaka wa Musulmin Myammar

kasashen da suka bai wa Musulmin Myammar agaji sun hada da Turkiyya da Bangladesh da Saudiyya, yayin da sauran takwarorinsu suka yi alkawarin ci gaba da kai agaji ga ’yan kabilar Rohingya da ake azabtar da su. kasashen Pakistan da Malesiya da Indonesiya su ne kan gaba wajen ganin an dauki matakin difulomasiya don shawo kan mawuyacin halin da wadannan al’umma suka smau kansu a kasarsu ta haihuwa.

Shi kuwa Ministan Harkokin Wajen Indonesiya Retno Marsudi ya gana da Aung San Suu Kyi da shugaban sojojin Myammar Hlaing a garin Naypyidaw don tursasa gwamnatin kasar ta yi kokarin shawo kan rikicin.

Ministocin kasashen da suka hada da Pakistan, Khawaja Muhammad Asif ya yi kira kan lallai “a dauki kwararan matakan da za su hana aukuwar irin wannan cin zarafi ga Muslimin Rohingya, inda takwaransa na Iran Jabad Zarif ya aike da sakon twirtter cewa: “Shirun da duniya ta yi kan keta haddin da ake yi Musulmin Rohingya ba abu ba ne mai kyau,  don haka a dauki matakin shawo kan kisan kare dangi – dole Majalisar dinkin Duniya ta shige gaba wajen tunkarar lamarin.”

Dubban Musulmin Chechnya ne suka taru a yankin da ke karkashin mulkin Rasha, inda suka yi zanga-zangar nuna alhini kan mummunan halin da Rohingya ke ciki.

Shugaban al’ummar Burma da ke Saudiyya ya yabi gwamnatin kasar kan tallafin da take ba su, musamman jin cewa Saudiyya za ta bayar da izinin zama kasar ga Rohingya miliyan guda, don haka Sheikh na Burma ya yabi Yarima Khaled Al-Faisal, wanda kafar sadarwar ta http://lifeinsaudiarabia.net ta ruwaito ya raba wa al’ummar takardar iznin zama a kasar.

kasar Turkiya  ce dai ta fara yin uwa da makarbiya wajen taimaka wa Musulmin Rohingya da ake azabtar da su a kasarsu ta haihuwa.

Alamu dai sun nuna gwamnatin Burma tana goyon bayan mabiya addinin Buddha, don haka ta nuna ko’in kula kan halin kan rikicin kasar. Bisa la’akari da hakan ya sanya ake ganin ana nuna wa Musulmi wariya. Firamiyinistan turkiyya Erdogan ya jadadda bukatar ganin kasar ta bude kafar shiga akai taimako.

Ma’aikatar harkokin wajen Hadaddiyar Daular Larabawa (UAE) tare da hadin kan kungiyoyin duniya sun jadadda aniyarsu ta kai kayan agaji ga tsirarun Musulmin Myammar, tare da tallafa musu don shawo kan mawuyacin halin da suka samu kan su a ciki. Sannan  sun yi kira ga Majalisar dinkin Duniya da ta daukio nauyi bayar da kariya ga Musulmin Rohingya, tare da hukunta duk wanda ke da hannun wajen kisan kare dangi da aka yi wa Musulmin Rohingya.