kasashen Musulmi sun yi Allah-wadai da harin Madina

Shugabannin kasashen duniya musamman na Musulmi sun ci gaba da yin Allah-wadai da harin da aka kai birnin Madina na kasar Saudiyya ranar Litinin.Shugabannin ciki har da na kasar Iran sun yi watsi da bambance- bambancen da ke tsakanin sun suka bayyana bakin cikinsu ga harin wanda aka kai kusa kabarin Manzon Allah (SAW).Minisatar Harkokin […]

kasashen Musulmi sun yi Allah-wadai da harin Madina
kasashen Musulmi sun yi Allah-wadai da harin Madina

Shugabannin kasashen duniya musamman na Musulmi sun ci gaba da yin Allah-wadai da harin da aka kai birnin Madina na kasar Saudiyya ranar Litinin.
Shugabannin ciki har da na kasar Iran sun yi watsi da bambance- bambancen da ke tsakanin sun suka bayyana bakin cikinsu ga harin wanda aka kai kusa kabarin Manzon Allah (SAW).
Minisatar Harkokin Wajen kasar Iran Jabad Zarif ya yi Allah-wadai da al’amarin, inda ya yi kira ga Musulmi su kasance tsintsiya madaurinki daya. “Babu wani wuri da ’yan ta’adda suka bari. Ahalil Sunnah da ’yan Shi’a duka abin zai ci gaba da shafar su, idan ba mu hada kanmu ba.”
Har ila yau, kasashen Malesiya da katar da Pakistan Jordan da Lebanon da sauransu su ma duka sun yi Allah-wadai da harin.
Akalla jami’an tsaro hudu ne suka rasa rayukansu da kuma dan kunar bakin waken da ya tayar da bam din.
Hotunan da gidan talabijin din kasar suka watsa sun nuna wata mota na ci da wuta yayin da hayaki ya tashi sama da gawar mutane biyu a gefen masallacin.
Wannan na zuwa ne bayan kai wani harin kunar bakin wake masallacin mabiya darikar Shi’a da ke birnin katif a gabashin kasar, an kuma kai wani harin kusa da ofishin jakadancin Amurka da ke Jeddah duk dai a ranar Litinin.
Kuma jami’an tsaro biyu ne suka mutu a harin Jeddah, kawo yanzu babu wata kungiya ko wanda ya dauki alhakin kai harin.
Majalisar koli ta Malaman kasar suka yi Allah-wadai da harin, tana cewa, ‘’Maharan sun karya duk wata dokar tsarkakakken waje.’’
Har yanzu dai babu wata kungiya da ta dauki alhakin kai harin, sai dai ana zargin kungiyar IS.