kasashen Musulmi sun zargi Iran da tallafa wa ta’addanci

Shugabannin kasashen Musulmi fiye da 50 sun zargi kasar Iran da tallafa wa ayyukan ta’addanci tare da tsoma baki a harkokin cikin gidan kasashen yankin ciki har da Siriya da Yemen.Shugabannin ciki har da Shugaban Iran Hassan Rouhani sun halarci taron kungiyar Hada kan kasashen (OIC) mai wakilai 57 don tattaunawa kan batutuwa da dama […]

kasashen Musulmi sun zargi Iran da tallafa wa ta’addanci
kasashen Musulmi sun zargi Iran da tallafa wa ta’addanci

Shugabannin kasashen Musulmi fiye da 50 sun zargi kasar Iran da tallafa wa ayyukan ta’addanci tare da tsoma baki a harkokin cikin gidan kasashen yankin ciki har da Siriya da Yemen.
Shugabannin ciki har da Shugaban Iran Hassan Rouhani sun halarci taron kungiyar Hada kan kasashen (OIC) mai wakilai 57 don tattaunawa kan batutuwa da dama da suka hada da na ’yan gudun hijira da Yakin Basasar Siriya ya haifar a taron day a gudana a Istanbul na kasar Turkiyya.
 “Taron ya soki tsoma baki da kasar Iran ke yi kan harkokin cikin gidan kasashen Musulmi ciki har da Bahrain da Yemen da Siriya da Somaliya da kuma yadda take ci gaba da tallafa wa ayyukan ta’addanci,” inji OIC a takardar bayan taro na karshe da ta fitar.
kungiyar ta nanata bukatar da ke akwai na “samun kyakkyawar dangantaka” a tsakanin Iran da sauran kasashen Musulmi ciki har da kauce wa yin amfani da karfi ko barazanar haka.
kasar Turkiyya wadda ta karbi shugabancin kungiyar OIC na tsawon shekara uku da kasar Saudiyya Arabia suna tare da Amurka a yakin da ake yi da ’yan bindiga a kasar Siriya a lokaci guda kuma suna adawa da Shugaba Bashar al-Assad, matsayin da yake sa su tsama da Iran, wadda take goyon bayan shugaban na Siriya.
 kasar Shi’a ta Iran a nata gefen tana goyon bayan ’yan tawayen Houthi da ke yakar gwamnatin shugaban da Saudiyya ke mara masa baya takaddamara da ta jawo mutuwar fiye da mutum dubu shida tun faruwarta a watan Maris din bara.
Takardar bayan taron ta zo ne kwana daya da Shugaban Iran Rouhani ya bukaci wakilan taro das u kauce wa duk wani bayani da zai kawo rarrabuwar kawuna. “Bai kamata wani sako da zai rura wutar rarrabuwa a tsakanin kasashen Musulmi ya fito daga wannan taro ba,” inji Rouhani kamar yadda gidan talabijin na kasar Iran ya ruwaito.

Sojoji sun kashe ’yan Boko Haram 30 a Borno

DAGA LARABA: Hanyoyin Dawo Da Martabar Karatun Tsangaya

Fitaccen ɗan kasuwar Kebbi, BLB ya rasu yana da shekara 54

Zaɓen Ondo: Ɗan takarar PDP ya garzaya kotu