Kasashen Turai na da hannu wajen cin zarafin mutane a Libya -Rahoto

Wani rahoto da kungiyar kare hakkin dan Adam ta duniya, wadda ake kira Amnesty International ta fitar, ya nuna cewa gwamnatocin kasashen Turai suna da hannu dumudumu a cikin harkallar cin zarafin ‘yan cirani da ‘yan gudun hijira da ke gudana a kasar Libiya. kungiyar ta yi wannan zargin ne a cikin wani rahoto da […]

Kasashen Turai na da hannu wajen cin zarafin mutane a Libya -Rahoto

Wani rahoto da kungiyar kare hakkin dan Adam ta duniya, wadda ake kira Amnesty International ta fitar, ya nuna cewa gwamnatocin kasashen Turai suna da hannu dumudumu a cikin harkallar cin zarafin ‘yan cirani da ‘yan gudun hijira da ke gudana a kasar Libiya.

kungiyar ta yi wannan zargin ne a cikin wani rahoto da ta fitar, inda ta kara da cewa a kokarinta na dakile kwararar bakin haure, kungiyar Tarayyar Turai tana taimaka wa “wani shirin cin zarafin” bakaken fata a gabar tekun Libiya kamar yadda BBC ta ruwaito.

Kudaden kungiyar Tarayyar Turai suna zuwa ga hukumomin da ke aiki da mayaka da kuma masu safarar mutane, kamar yadda rahoton ya nuna.

Kuma rahoton ya nuna cewa kungiyar Tarayyar Turai ta bayar da jiragen ruwa da horaswa da kuma kudi ga jami’an tsaron gabar tekun Libiya.