Kasashen Turai ne ke samar wa Boko Haram kudi da makamai – Kungiyar SHAC
Wata kungiyar mai suna Sabe Humanity Adbocacy Center (SHAC) ta nanata zargin da take yi wa kasar Faransa cewa ita take daukar nauyin kungiyar Boko Haram ta hanyar tallafa musu da kudi da samar wa kungiyar miyagun makamai don su ci gaba da aiwatar da ayyukansu na ta’addanci a kasar nan. Kungiyar ta bayyana haka […]
Wata kungiyar mai suna Sabe Humanity Adbocacy Center (SHAC) ta nanata zargin da take yi wa kasar Faransa cewa ita take daukar nauyin kungiyar Boko Haram ta hanyar tallafa musu da kudi da samar wa kungiyar miyagun makamai don su ci gaba da aiwatar da ayyukansu na ta’addanci a kasar nan.
Kungiyar ta bayyana haka ne a wani taron manema labarai da ta kira a Abuja a shekaranjiya Laraba kamar yadda jaridar Aljazeera Nigeria ta ruwaito.
Sakataren Kungiyar Kwamared Ibrahim Abubakar wanda ya yi tsokaci kan rahoton da ke cewa kungiyar Boko Haram ta samu manyan makamai da jirage marasa matuka ya zargi Faransa da tallafa wa kungiyar.
Kungiyar SHAC ta nuna wa kasar Faransa da kawayenta yatsa a kan wannan sabon makirci, musamman ganin yadda tarihi ya nuna yadda dama wasu kasashen Turai suke nukura da kasancewar Najeriya kasa.
Tunda yake Faransar ba ta ce uffan ba, kungiyar ta yi mata kalubale inda ta ce “Ki fada wa duniya gaskiya wane ne ke ba Boko Haram makamai tunntuni.”
Kungiyar daga nan ta yi kira ga Rundunar Sojin Najeriya ta ci gaba da kara kaimi kan yakin da take yi, sannanta bukaci kasashen da wannan rikici ya shafa su hada karfi da karfe don ganin sun sare sarkar bautar da har yanzu take a kafafuwansu wacce ’yan mulkin mallaka suka daure su da ita.