Kasashen Turai za su aika wa Ukraine makamai

EU za ta yi taron gaggawa kan bukatar amsa kiran Ukraine na karfafa ba ta tallafin soji.

Kasashen Turai za su aika wa Ukraine makamai

Shugaban Faransa Emmanuel Macron

Fadar shugabancin Faransa ta ce gwamnatin kasar za ta aike da karin kayan aikin soji, da kuma man fetur zuwa Ukraine, domin taimakawa wajen yaki da mamayar da Rasha ta yi mata.

Sanarwar ta kuma ce Faransar za ta laftawa Rasha karin takunkuman karya tattalin arziki.

A cewar Fadar Elysee, sabbin takunkumin za su kunshi “matakan kwace kadarori da kuma kudaden manyan jami’an gwamnatin Rasha.

Ministocin Harkokin Wajen na Kungiyar Tarayyar Turai EU za su gudanar da taro a ranar Lahadi kan bukatar amsa kiran Ukraine na karfafa ba ta tallafin soji da kuma tsaurara takunkumi kan Rasha dangane da afka matan da ta yi da yaki.

Tattaunawar gaggawar ya zo ne jim kadan bayan da Jamus ta janye adawar ta na hana Rasha amfani da tsarin bai daya tsakanin kasa da kasa na hada-hadar sadarwar bankunansu da ake kira da SWIFT, daya aga cikin manyan bukatun kasar Ukraine.

Kazalika, Jamus ta kuma amince da bai wa Ukraine tallafin makamai, abinda ke nufin ta sauya manufar da ta dade tana amfani da ita, na haramta fitar da makamai zuwa yankunan da ake rikici.

Ita ma gwamnatin Sweden ta sanar cewa za ta aika wa Ukraine kayan yaki da sauran tallafi.

Da take sanar da matakin, Firaminista Magdalena Andersson ta ce wannan ne karon farko da Sweden ke tura wa wata kasa da ke yaki kayan fada tun bayan 1939 da Tarayyar Soviet ta afka wa Finland.

Ta ce kayan za su kunshi makaman harbe tankoki 5,000 da riguna masu silke 5,000 da hular kwano 5,000 da kuma kunshin harsasai 135,000.

“Na fahimci cewa tsaronmu shi ne kawai idan muka taimaka wa Ukraine ta kare kanta daga harin Rasha,” a cewarta.