Kashamu: Abin da Obasanjo ya fada tsabagen munafunci ne – Ebute

Tsohon Shugaban Majalisar Dattawa a Jamhuriyya ta Uku Sanata Ameh Ebute, ya zargi tsohon Shugaban kasa Olusegun Obasanjo da munfunci da rashin gaskiya kan kalaman da ya rika yi game da ziyarar fa shugabannin Jam’iyyar PDP suka rika kai masa da niyyar magance rikice-rikicen da ke addabar jam’iyyar a yankin Kudu maso Yamma. Sanata Ebute, […]

Kashamu: Abin da Obasanjo ya fada tsabagen munafunci ne – Ebute
Kashamu: Abin da Obasanjo ya fada tsabagen munafunci ne – Ebute

Tsohon Shugaban Majalisar Dattawa a Jamhuriyya ta Uku Sanata Ameh Ebute, ya zargi tsohon Shugaban kasa Olusegun Obasanjo da munfunci da rashin gaskiya kan kalaman da ya rika yi game da ziyarar fa shugabannin Jam’iyyar PDP suka rika kai masa da niyyar magance rikice-rikicen da ke addabar jam’iyyar a yankin Kudu maso Yamma.

Sanata Ebute, wanda yanzu shi ne Uba kuma Shugaban Jami’ar Yin Karatu daga Gida (National Open Unibersity of Nigeria -NOUN), ya bayyana haka ne a wata budaddiyar wasika da ya aike ga Ci Obasanjo, inda ya ce ya zame masa dole ya aika wasikar tunda abin da zai yi magana yana gaban jama’a.
Ya ce, abin da ya sa Obasanjo ke fushi da jam’iyyar kamar yadda ke kunshe a cikin sanarwar labarai da ya bayar “babban daba wa cikinsa wuka ne.”
A makon jiya ne Cif Obasanjo ya ce daya daga cikin matsalaolinsa da shugabannin Jam’iyyar PDP shi ne nada Buruji Kashamu a matsayin jagoran jam’iyyar a yankin da ya fato.
A martanin Cif Ebute ya ce, “Tare da girmamwa, wannan bayani naka na nuna tsabagen munafunci da tantagaryar karya. Duk da cewa ba ka ambaci sunan mutumin da kake magana ba, abu ne a fili cewa wanda ake zargi da safarar miyagun kwayoyi ba wani ba ne face Yarima Buruji Kashamu, mutumin da kake da cikakkiyar alakar siyasa da shi har zuwa shekarar 2011.”
Ya ce, “Ina son tunatar da kai cewa, tsohon Gwamnan Jihar Ogun, Otunba Gbenga Daniel ya kwace iko da PDP a shekarar 2008/2009, kuma wannan “falken miyagun kwayoyin” ne ka hada hannu da shi kuka kafa wata sakatariyar jam’iyyar kuka shigar da kara a kotu. Kuma wannan mutum ne ya samo hukuncin kotu da y aba bangarenku hallaccin da uwar Jam’iyyar PDP ta kasa ta amince da ku a daidai lokacin da ake tunkarar zaben 2011.”
Cif Ebute ya ce, ’yar tsohon Shugaban kasa, Iyabo Obasanjo ta yi aiki kafada da kafada da Kashamu domin ya tsare tare da kare yunkurin dusashe hasken siyasar mahaifinta a jiharsa, kuma a wannan lokaci ne Buruji ke yawan ziyarta gidan Obasanjo na kan tsauni da ke Abeokuta inda ake tarbarsa da bukukuwa. Ebute ya tambayi Obasanjo cewa me yake fada wa “abokansa na kasashen waje” a wancan lokaci kan Kashamu?