Kashe attajiri ya haifar da hatsaniya a garin Jega
Rikici tsakanin ’yan sanda da al’ummar gari a Jega da ke Jihar Kebbi ya yi sanadiyyar salwantar rayukan mutum biyar a yayin da 26 suka samu raunuka, suna kwance a asibitin Sa Yahaya da ke Birnin Kebbi da kuma babban asibitin garin Maiyama. Wani mutum da al’amarin ya faru a gabansa, mai suna Lirwanu Sani […]
Rikici tsakanin ’yan sanda da al’ummar gari a Jega da ke Jihar Kebbi ya yi sanadiyyar salwantar rayukan mutum biyar a yayin da 26 suka samu raunuka, suna kwance a asibitin Sa Yahaya da ke Birnin Kebbi da kuma babban asibitin garin Maiyama.
Wani mutum da al’amarin ya faru a gabansa, mai suna Lirwanu Sani Jega, ya shaida wa Aminiya sanadiyyar wannan rikici, inda ya ce a ranar Asabar da ta gabata, da misalin karfe 8:30 na dare wasu ’yan bindiga suka je shagon dan kasuwa, Alhaji dankane Jega, inda suka harbe shi ya mutu kuma suka kwashe kudi kimanin Naira milyan 40.
Kamar yadda ya ce: “A lokacin da ’yan bindigar suka isa shagon; an kai rahoto ofishin ’yan sanda domin babu nisa tsakaninsa da ofishin ’yan sanda amma DPO na yankin, Aliyu Yusuf bai tura ’yan sanda a lokacin da aka kawo masa rahoto ba sai bayan dogon lokaci da wucewar ’yan bindigar,” inji shi.
Ya ci gaba da cewa: “Da safe bayan an kai mamacin makabarta da misalin karfe tara, matasa na dawowa suka shigo cikin gari sai suka fara fadin ‘ba ma son DPO, ba ma son ciyaman na karamar hukuma.’ To daga nan ne fa sai zanga-zanga ta fara, sai matasa suka fara kona tayoyi a kan hanyoyi. Daga nan ne fa sai ’yan sanda suka tarwatsa su, suka ci gaba da bude wa jama’a wuta, suna ta harbi. A nan take dai suka kashe mutum hudu da kuma wata mahaukaciya daya.”
A sanadiyyar wannan al’amari dai an kona ofishin ’yan sanda na garin da kuma gidajen ’yan sanda guda biyu.
Aminiya ta tambayi Kwamishinan ’yan sandan Jihar Kebbi, Alhaji Ishaku Barau Ningi, ko me zai ce game da aukuwar wannan al’amari? Ya tabbatar wa Aminiya aukuwar wannan al’amari kuma ya yi kira ga al’ummar Jihar Kebbi da su zauna lafiya kamar yadda akan san jihar a sahun gaba wajen zaman lafiya. Ya ce jama’a su bar daukar wa kansu doka.
Kwamishinan ya ce zarge-zargen da ake wa DPO, ya ba da izinin a canza shi a kawo wani ba tare da bata lokaci ba, kuma jama’a su fito su ci gaba da gudanar da harkokinsu na yau da kullun.
Shi ma Shugaban karamar Hukumar Jega, Alhaji Haruna Haruna Maijega ya yi kira ga al’umma da su kasance masu bin doka da oda kuma ya ce kowa ya san mutanen Jega da zaman lafiya. Y ace su dauki wannan al’amari a kan kaddarar da Allah Ya rubuta sai ta faru.