Kashe fararen hula: Amnesty ta nemi a tuhumi sojoji da ’yan Boko Haram
kungiyar Kare Hakkin dan Adam ta Duniya (Amnesty International) ta bukaci kasashen duniya su tilasta a tuhumi sojojin Najeriya da ’ya’yan kungiyar Boko Haram da laifuffukan cin zarafin dan Adam, inda ta zargi bangarorin biyu da hallaka fararen hula.Wani rahoto da kungiyar ta fitar a farkon wannan mako ne ya bayyana haka inda ya zargi […]
kungiyar Kare Hakkin dan Adam ta Duniya (Amnesty International) ta bukaci kasashen duniya su tilasta a tuhumi sojojin Najeriya da ’ya’yan kungiyar Boko Haram da laifuffukan cin zarafin dan Adam, inda ta zargi bangarorin biyu da hallaka fararen hula.
Wani rahoto da kungiyar ta fitar a farkon wannan mako ne ya bayyana haka inda ya zargi sojoji da kashe mutum 600 bayan da ’yan Boko Haram suka kai hari ga barkin soja na Giwa da ke Maiduguri.
kungiyar wadda ta rika kafa hujja da shaidun da suka ga abin da ya faru ta ce, bayan kai harin tsararrun da suka gudu a Maiduguri an kama su kuma aka rika kashe su.
Hukumomin soja ba su mayar da martani kan zargin ba, sai dai a baya sun rika musanta rahoton na Amnesty.
Kimanin mutum 1,5000 aka kashe a farkon wata uku na bana, kuma rabin wadanda aka kashen fararen hula ne inji kungiyar.
daruruwan mayakan Boko Haram ne suka kai hari ga barikin soja na Giwa da ke Maiduguri a ranar 14 ga Maris. Kuma hukumomin soja sun fadi a lokacin cewa sun samu nasarar dakile harin inda suka kashe mahara da dama ta amfani da sojan sama da na kasa.
Wani ganau ya shaida wa Amnesty cewa ’yan bangar da ake kira sibiliyan JTF sun kama daruruwan wadanda suka gudu daga tsaro a barikin. “Na ga sojoji suna ce wa mutanen su kwanta a kasa. Kuma an samu ’yar takaddama a tsakanin sojojin da sibiliyan JTF. Sai sojojin suka yi waya, bayan mintoci kadan sai suka fara harbin mutanen da ke kwancen. Na kirga gawarwakin mutum 198 da aka kashe a wannan wurin duba motoci,” inji shaidar.
Amnesty ta ce hotunan setilayit sun nuna manyan kabarurruka uku da aka binne mutane a sashin birnin.
Galibi ana tsare wadanda ake zargi ’yan Boko Haram ne da aka kama a barikin Giwa, kuma kungiyoyin kare hakkin dan Adam sun ce daruruwa sun mutu ko an rika gana musu azaba, zargin da sojojin suka musanta.
Boko Haram sun sake wani faifan bidiyo kan harin inda suka nuna dimbin mutane suna ficewa daga barikin.
Amnesty ta ce dukan bangarorin biyu suna keta dokokin duniya, kuma ta bukaci Majalisar dinkin Duniya ta taimaka wajen bincikar yiwuwar aikata laifuffukan yaki da kuma cin zarafin dan Adam.
“Hakika ta’addancin da Boko Haram ke aikatawa yana da daga hankali, tare firgitarwa da sanya tsoro,” inji Netsanet Belay ta Amnesty. Sai dai ta ce: “Wannan ba zai zama lasisin wuce gona da iri wajen mayar da martani kamar yadda jami’an tsaron Najeriya suke yi ba.”