Kashe-kashe: Abin jiya na neman dawowa a Kudancin Kaduna
Ga dukkan alamu abin jiya yana neman dawowa a Kudancin Jihar Kaduna inda ake samun kashe-kashen jama’a. Ana cikin jimamin harbe wadansu ’yan sanda da mahara suka yi a hanyar Fadan Karshi da ke Karamar Hukumar Sanga ne, sai aka sake samun wani sabon harin inda aka kashe wadansu manoma biyu a kauyen Agon da […]
Ga dukkan alamu abin jiya yana neman dawowa a Kudancin Jihar Kaduna inda ake samun kashe-kashen jama’a. Ana cikin jimamin harbe wadansu ’yan sanda da mahara suka yi a hanyar Fadan Karshi da ke Karamar Hukumar Sanga ne, sai aka sake samun wani sabon harin inda aka kashe wadansu manoma biyu a kauyen Agon da ke Karamar Hukumar Sangar. Lamarin ya faru ne da misalin karfe hudu na ranar Alhamis din makon jiya, inda lamarin ya jefa mutanen kauyen cikin zullumi da firgici.
Da yake yi wa Aminiya bayani kan sabon harin, Shugaban Karamar Hukumar Sanga wanda Mataimakinsa Alhaji Abba Abubakar Umar ya wakilta ya ce mutanen da aka kashe su ne; Monday Kure da Emmanuel Madaki wadanda dukkansu manoma ne, kuma hakan ya jefa mutane cikin damuwa.
Ya ce bincike na ci gaba da gudana don zakulo masu neman hautsina garin da maido da hannun agogo baya a Kudancin Kaduna.
A karshe ya shawarci jama’ar yankin su mayar da hankalinsu wajen lura da duk wani bakon lamari da ke wakana a garuruwansu.
Wani harin wanda ya nemi tayar da fitina ya sake faruwa mako guda bayan wannan a lokacin da wadansu da ake zargin barayin shanu ne suka hallaka wani mai suna Yanbuwat Gimba a kan hanyarsa ta zuwa gonarsa ta kwakwa don debo giyar bammi, inda suka yi masa kisan gilla tare da tattara wasu shanu bakwai na wani dan banga mai suna Boniface Yakubu.
Wannan lamari ya faru ne a kauyen Agban-Kagoro da ke hanyar zuwa Gidan Waya a Karamar Hukumar Kaura, sai dai tuni aka kama su tare da iza keyarsu zuwa ofishin ’yan sanda na garin Kafanchan a Karamar Hukumar Jama’a.
Kakakin Rundunar ’Yan sandan Jihar Kaduna, ASP Suleiman Abubakar ya tabbatar da faruwar lamarin cikin wata takardar manema labarai da ya fitar kwana daya bayan faruwar lamarin.
Shi ma da yake karin hasken, Shugaban Riko na Karamar Hukumar Kaura Dokta Bege Katuka ya ce bayan faruwar lamarin, wadansu fusatattu sun nemi tayar da fitina inda suka bazama cikin daji don neman daukar fansa a kan Fulani makiyaya, wanda hakan ya sa suka kashe wadansu yaran makiyaya uku da suka tarar a cikin daji tare kashe shanu biyu.
“Sai dai cikin makiyayan da aka kashe biyu daga ciki mutanen Ganawuri ne kuma Kiristoci ne daya ne a ciki Bafulatani Musulmi kuma dukkansu suna karkashin kulawar wani Bafulatani ne da ke garin Tafan Gida,” inji shi.
A Karamar Hukumar Kachiya ma an gano gawar wani matashi mai suna Mujtaba Saminu wanda aka kona shi kurmus bayan kwana biyar da bacewarsa.
Shi dai wannan matashi mai kimanin shekara 28 ya rasu ya bar matarsa guda daya da cikin wata biyu. Wani dan uwansa kuma mai magana da yawun dangin mamacin, Lauya Nasiru Buhari Dabo ya shaida wa Aminiya cewa dan uwansa ya tafi wani kauye da ake kira Maro a ranar Juma’a inda wadansu suka yi yunkurin kashe shi amma Allah Ya kubutar da shi.
Ya ce Mujtaba fitacce ne a kasuwar tunda ya kwashe fiye da shekara 10 yana zuwa cin kasuwa a kauyen “Amma da ya dawo gida bai fada mana ba. Ranar Lahadi ya sake fita zuwa kauyen Chibiya a kan babur kuma ya gama cin kasuwa har ya bai wa direba wasu kaya ya kawo masa gida amma shiru sai ranar Talata kawai aka kira mu aka shaida mana cewa bai kwana a gida ba, tunda ba a gida daya muke ba. Daga nan wani kawunmu da ya baro shi a can da misalin karfe biyar ya kira kasuwar ya tambaya aka shaida masa ya bar kasuwar a babur dinsa da buhun gyada,” inji shi.
Ya ce da ya je bai same shi ba kuma ya yi ta kiran lambobin wayarsa suna shiga amma ba a dauka sai daga baya wasu kabilu suka dauka suka ce masa su Fulani ni shi ne ya dawo ya shaida wa ofishin ’yan sanda da na DSS da ke Kachiya. “Da muka ji shiru ne ranar Laraba muka je barikin sojin sama da ke Kachiya muka shaida musu kuma nan da nan suka raka mu bincikawa saboda irin haka ya sha faruwa kuma sun sha bincikawa ana gano gawarwaki mutane,” inji shi.
Ya ce sun je ranar Laraba ba su samu komai ba har zuwa Alhamis amma sai ga labari daga wani dan garin Kachiya da ya rage wa wata mata hanya a kan babur inda take shaida masa cewa su binciki wani wuri a Chibiya saboda ta ji wani ihu da misalin karfe biyar da rabi na yammacin ranar da ake zaton an kashe shi.
“Sai muka sake dunguma da sojojin sama a safiyar ranar Juma’a zuwa wurin inda muka tarar har an kona gawarsa, mun gane shi ne ta hanyar gefen rigarsa kawai,” inji shi.
Ya ce suna matukar kokari domin ganin sun tsare rayukan duk wani dan kabilar Adara da ya shigo garin Kachiya amma su kuma ba a tsare rayukan ’yan uwansu da wata harka ta bi da su ta wadancan unguwanni.
Ya yi kira ga Gwamnan Jihar Kaduna da Kwamishinan ’Yan sanda su taimaka ta hanyar runduna ta musamman da za su zo su yi bincike ba tare da shugabannin ’yan sanda da na kananan hukumomin Kachiya da Kajuru ba.