Kashe-kashen jama’a: Mu tuba ga Allah domin samun mafita (1)
Huduba ta Farko: Godiya ta tabbata ga Allah Masani Mai hikima, Ya halicci halittu kuma Ya jarrabe su. Ya sanya sashinsu ya zama jarrabawa ga sashi.“Kuma kamar haka ne Muka fitini sashinsu da sashi, domin su ce. “Shin, wadannan ne Allah Ya yi falala a kansu daga tsakaninmu?” Shin, Allah bai zama Mafi sani ba […]
Huduba ta Farko:
Godiya ta tabbata ga Allah Masani Mai hikima, Ya halicci halittu kuma Ya jarrabe su. Ya sanya sashinsu ya zama jarrabawa ga sashi.
“Kuma kamar haka ne Muka fitini sashinsu da sashi, domin su ce. “Shin, wadannan ne Allah Ya yi falala a kansu daga tsakaninmu?” Shin, Allah bai zama Mafi sani ba ga masu godiya?” An’am:53.
“…Kuma mun sanya sashin mutane fitina ga sashi, Mu gani, shin ko za ku yi hakuri? Kuma Ubangijinka Ya kasance Mai gani” (Furkan:20).
Muna godiya ga Allah (SWT) a kan jarrabawarSa, kuma muna gode maSa a kan ni’imominSa. Muna rokonSa Ya ba mu ikon cin jarrabawar da duk Ya jarabe mu da ita, tare da tabbatuwa da dugaduganmu a kan addininSa da umurninsa. Muna rokon Allah Mai kowa Mai komai, Ya sa mu rabauta da samun yardarSa da tsira daga azabarSa. Domin lallai azabarSa idan ta sauka, babu mai iya tunkude ta idan ba Shi ba.
Kuma ina shaidawa lallai babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, Shi kadai Yake, ba Ya da abokin tarayya. Ya yi wa muminai daga cikin bayinSa alkawari cewa, duk runtsi, duk tsanani, duk wahala, lallai su ne masu cin nasara daga karshe. Ya shiryar da su tafarki madaidaici, kuma Ya umurce su da yin hakuri, domin da shi ne nasara da daukaka suke samuwa.
“Kuma mun sanya jagorori daga cikinsu, suna shiryarwa da umurninMu, a lokacin da suka yi hakuri, kuma sun kasance suna yin yakini da ayoyinmu.” (Sajadah:24).
Kuma ina shaidawa lallai Annabi Muhammad (SAW), bawanSa ne, kuma ManzonSa ne. Ya isar da sakon Allah matukar isarwa. Kuma ya yi hakuri a kan cutarwar masu cutar da shi daga kafirai, Yahudawa da munafukai daga cikin Musulmi, har ya ci nasara, ya samu daukaka. Addininsa ya rinjaya, ambatonsa ya daukaka mabiyansa suka buwaya, Allah Ya kunyata makiyansa. Tsira da amincin Allah da albarkokinSa su kara tabbata a gare shi, da iyalansa da sahabbansa da mabiyansa har zuwa Ranar Sakamako.
Bayan haka, ya ku bayin Allah! Lallai ku ji tsoron Allah, kuma ku yi maSa da’a. Sannan ku yawaita bautarSa da ambatonSa. Ku yi riko da igiyarSa kada ku rarraba, ku riki addininSa da karfi a duk halin da kuka samu kanku a ciki na jarrabawa. Matukar kuna a kan gaskiya, to ba za ku bata ba. Kuma lallai mu sani, dukkanmu abin tambaya ne a kan yadda muka gudanar da rayuwarmu a wannan duniya.
Ya ku mutane! Lallai duk wani mutum mai imani, idan ya yi dubi da idon basira ya kalli irin abin da ke faruwa ga ’yan uwanmu da ke jihohin Barno, Yobe da Adamawa, ya san cewa lallai wadannan bayin Allah suna cikin wani irin mawuyacin hali na tsanani da takura daga azzalumai. Suna cikin wani irin mummunan yanayi da suke bukatar dauki daga gare mu da taimakonmu da agajinmu koda na addu’o’i ne. Ta inda ake bi gari-gari, kauye-kauye, unguwa-unguwa, lungu-lungu, sako-sako ana ta hallaka su da kone musu gidaje da dukiyoyinsu babu gaira babu dalili, ba su san hawa ba, ba su san sauka ba, haka siddan.
Allah Sarki! Babban malami, Abul Bakaa Ar-Randiy ya kasance yana fada a wasu baituka nasa:
“Da irin wannan ne ya kamata zuciya ta zubar da hawaye don bakin ciki,
Idan ya kasance a cikin zuciyar akwai Musulunci da imani.”
Ya ku bayin Allah! Lallai farkon abin da muke son shaida wa ’yan uwanmu da ke cikin wannan hali na damuwa a Barno da Yobe da Adamawa da sauran wurare, shi ne su yi hakuri su zama masu juriya a kan wannan jarrabawa da Allah (SWT) Ya jarrabe su da ita. Muna nan muna ta yi musu addu’o’i da alkunuti. Sannan don Allah sauran al’ummar Musulmin Najeriya, mu kara zage dantse wurin yawaita yin addu’o’i a kan wannan al’amari. Mu yi ta yin alkunuti a sallolinmu na hamsu salawati a masallatanmu da Sallar Wutiri da muke yi a gidajenmu a tsakiyar dare. Insha Allahu mun yi imani da Allah, wallahi wannan al’amari zai zama tarihi. Domin Allah (SWT) ne kawai ba Ya da farko ba Ya da karshe. Amma duk abin da ba Allah ba ne, to yana da farko, kuma tunda ya yi farko to dole ne zai yi karshe.
Ya ku bayin Allah! A yau ina Fir’auna? Allah (SWT) Ya ba mu labari a cikin LittafinSa Mai girma irin yadda Fir’auna ya kasance yana yanka bayin Allah. Ya yanka ’ya’ya maza na Bani Isra’ila dubbai wadanda Allah ne kawai Ya san iyakarsu, ya yanka maza ya bar mata. To amma a yau Fir’auna ya gama tsiyatakunsa an wayi gari ya zama tarihi. Babu mutunci a nan duniya, kafin ya hadu da mummunar azaba a Lahira.
Sannan ya kamata al’ummar Musulmi su tuna, lallai duk wannan kashe-kashe da zubar da jinin bayin Allah da ke faruwa a Arewacin Najeriya da ma duniya baki daya, abu ne da Manzon Allah (Tsira da Amincin Allah su kara tabbata a gare shi) ya yi bayanin faruwarsa, har ma ya sanya shi a cikin jerin alamomin tashin Alkiyama. Ya nuna cewa da zarar kashe-kashe da zubar da jini sun yawaita, to, alamu ne da ke tabbatar da kusantowar Alkiyama.
Imamu Muslim ya ruwaito Hadisi, daga Abu Huraira (Allah Ya kara masa yarda), ya ce: “Lallai Manzon Allah (SAW) ya ce: “Lallai Alkiyama ba za ta tsayu ba, har sai an samu yawaitar ‘Al-Harju’ sai sahabbai suka tambayi Manzon Allah, mene ne Al-Harju?’ Sai ya ce, “shi ne kisa, shi ne kisa.”
A wata ruwaya ta daban daga Imamu Muslim din, kuma shi ma daga Hadisin Abu Huraira, Annabi (SAW) ya ce: “Ina rantsuwa da wanda rayuwata take hannunSa (Allah)! Duniyar nan ba za ta kare ba, har sai wata rana ta zo wa mutane da mutumin da aka kashe bai san dalilin da ya sa aka kashe shi ba. Wanda ya yi kisan ma bai san akan wane dalili yayi kisan ba”.
Ya ku bayin Allah! Idan mun yi dubi da idon basira a kan wadannan maganganu na Annabi (SAW), za mu ga cewa duk abin da ya yi bayanin faruwarsa shi ne yake faruwa a yau. Kuma hakika, kofar kashe-kashe da zubar da jini ta bude ne tun daga lokacin da wasu ’yan ta’adda suka kashe Halifan Manzon Allah (SAW) na Uku, wato Usman (R.A). Tun daga wancan lokaci har zuwa yau din nan wannan kofa tana nan a bude. Yake-yake da dama sun auku a duniya wadanda babu wani kwakkwaran dalili na takalo su ko faruwarsu. Wadannan yake-yake sun Jawo asarar rayukan miliyoyin mutane. Makamai na fitar hankali a yau sun yadu a duniya, duk ba don komai ba sai don taimaka wa wadancan yake-yake.
Ga misalin kadan daga cikin yake-yaken da suka gudana a duniya, domin ka kara tabbatarwa, tare da kara yin imani da gaskiyar Manzon Allah (SAW):
1. Yakin Duniya na Farko. An yi asarar rayuka sama da miliyan 15 a cikinsa.
2. Yakin Duniya na Biyu. An yi asarar rayuka sama da miliyan 55 a cikinsa.
3. Sai Yakin Biyatnam. Wanda shi ma miliyoyin mutane sun mutu a cikinsa.
4. Sai Yakin Basasa (na cikin gida) a Rasha. An yi asarar sama da mutum miliyan 10.
5. Sai Yakin Basasar Asfaniya (Spain). Shi ma ya ci rayukan mutum sama da miliyan 12.
6. Sai Yakin da aka yi tsakanin Iraki da Iran (Yakin Khalij na farko). Miliyoyin mutane sun mutu.
7. Sai yakin da aka yi a Iraki. Ya ci ran dan Adam sama da miliyan daya. Ban da kashe-kashe da zubar da jinin da ke gudana yau a kasar (Iraki).