Kashe-kashen jama’a: Mu tuba ga Allah domin samun mafita (2)

Ya ku bayin Allah! Idan kun duba duka duniyar haka take, kafin mu dawo nan gida Najeriya.Idan ka kalli abin da ke faruwa a kasashen Musulmi a yau, na kashe-kashe da zubar da jini da yake-yake, wallahi al’amarin zai tada hankalin duk wani mai imani. Kuma duk inda ka duba, za ka ga da hannun […]

Kashe-kashen jama’a: Mu tuba ga Allah domin samun mafita (2)

Ya ku bayin Allah! Idan kun duba duka duniyar haka take, kafin mu dawo nan gida Najeriya.
Idan ka kalli abin da ke faruwa a kasashen Musulmi a yau, na kashe-kashe da zubar da jini da yake-yake, wallahi al’amarin zai tada hankalin duk wani mai imani. Kuma duk inda ka duba, za ka ga da hannun Turawa a ciki. A inda za su samu wasu rubabbun Musulmi wawaye wadanda ba sa kishin al’ummarsu, su yi ta amfani da su, suna zubar da jinin ’yan uwansu. Da ma su makiya Musulunci da Musulmi ba su kaunar ganin an samu zaman lafiya a tsakanin Musulmi. Ta inda za su yi ta taimakawa tare da ruruta wutar rikicin bangaranci da bambance-bambance a tsakanin al’umma. Wannan shi ne yake faruwa a kasashe irin su: Falasdinu da Masar da Libiya da Iraki da Siriya da Pakistan da Afghanistan da sauransu. Wanda mu ma an wayi gari a yau, ba mu tsira daga irin wadancan makirce-makircen ba. An wayi gari ana amfani da wasu daga cikinmu ana cutar da mu. To, koma dai mene ne, muna da cikakken yakinin cewa, gaskiya ce za ta yi nasara, in Allah Ya yarda. Kuma sai Allah (SWT) sai ya kunyata duk wani mai mummunar manufa a kan wannan al’umma.
Duk wannan al’amari ya ku ’yan uwa! Wallahi yana kara tabbatar mkna da gaskiyar Manzon Allah (SAW) da ya ce kashe-kashe za su yawaita, kuma mutane za su yi ta kisan juna ba tare da sanin dalilin yin hakan ba.
Allah Ya albarkace ni da ku a cikin bin Alkur’ani da Sunnah, Ya amfanar da ni da ku da abin da ke cikinsu na ayoyi da zikirori na hikima, ina fadar wannan magana tawa, ina mai neman gafarar Allah ga kaina da ku da dukkanin Musulmi daga dukkan zunubi da kuskure. Ku nemi gafararSa, lallai Shi Mai gafara ne Mai jinkai.

Huduba ta Biyu:
Godiya da yabo ga Allah (SWT):
Bayan haka ya ku bayin Allah! Lallai wallahi ya zama wajibi a gare mu, muji tsoron Allah. Mu kakkabe hannayenmu daga saba wa Allah. Daga shugabanni har mu mabiya, mu ji tsoron Allah. Yin haka zai sa Allah Ya tausaya mana Ya fitar da mu daga cikin halin da muka samu kanmu a ciki.  A yau, mu duba mu ga yadda sabon Allah da zunubai da laifuffuka iri-iri suka mamaye wannan al’umma. Kama daga sata (da duk nau’o’inta) da shan giya da shaye-shayen abubwan maye da zina da karya da luwadi da madigo da karya da yaudara da hassada da giba da annamimanci da gulma da keta da gaba da kin juna da cuta da yi wa juna sharri da cin duga-dugin juna da shirka da tsafi da kungiyoyin asiri da bin bokaye da malaman tsibbu da cin hanci da rashawa da rikice-rikicen kabilanci da na addini da bata lokaci wurin wasannin banza marasa amfani da rashin tsoron Allah a duk al’amuranmu da sauransu. Ya kamata mu sani, matukar muna cikin wadannan miyagun ayyuka munana, to Allah ba zai taba amsa addu’o’inmu da kunutinmu ba. Sannan matukar ba doka, kuma ba tsayar da adalci a cikin al’umma, to samun zaman lafiya zai yi wahala. Allah Ya kiyaye, amin. Matukar kuwa ba zaman lafiya, to, mun san ci gaba mai ma’ana zai wahala, Allah Ya tsare. Sannan mun manta cewa Allah fa Ya shaida mana cewa Shi Mai iko ne a kan Ya saukar mana da azaba, ko kuma Ya saukar mana da rarrabuwa da sabani a tsakaninmu mu yi ta yakar juna, muna kisan kanmu da kanmu.
Allah Ta’ala Ya ce: “Ka ce: “Shi (Allah) Mai iko ne a kan Ya aiko da wata azaba a kanku, daga samanku, ko kuwa daga karkashinku, ko kuwa ya rarrabaku kungiyoyi, (ku yi ta yakar juna, kuna kisan juna), kuma Ya dandana wa sashinku masifar sashi. Ka duba yadda Muke sarrafa ayoyi, tsammanin su suna fahimta!” An’am:65.
Ya ku bayin Allah masu girma! Don Allah mu koma ga tafsiran manyan malaman tafsiri na duniya mu ga yadda suka fassara wannan aya, wallahi za mu sha mamaki. Ba zan kawo bayanan malaman tafsirin a wannan huduba tawa ba, don gudun tsawaitawa.  Amma ya kamata mu duba tafsirin wannan aya ta 65 a cikin Suratul An’am a tafsirai kamar na: Ibnu Jarir At- Tabariy da Al-Khurdabiy da Ibnu Kasir da Tafsirin Bagawiy da Aysarut-Tafaasir da Tafsirin Ibnu Sa’adiy da Tafsirul Munir da Tafsirin kasimiy da Tafsirin Raddul Azhan Ila Ma’anil kur’an na babban malaminmu, Ash-Sheikh Abubakar Mahmud Gumi (Allah Ya jikansa da rahama), insha-Allah dan uwa za ka gamsu da jawabin da na yi maka na musibar da ta auka wa al’ummar nan.
Ya ku bayin Allah! Lallai ku sani malamai sun yi bayani ga al’umma cewa, na daga cikin alamomin tashin Alkiyama da Annabi (SAW) ya bayyana, lallai Allah ba zai saukar wa wannan al’umma yunwa da fari ba, kuma ba zai taba dora makiyanmu a kanmu ba, face har sai mun koma muna kisan junanmu. Kuma Annabi (SAW) ya tabbatar da lallai hakan zai faru, kuma ma faruwarsa alama ce daga alamomin tashin Alkiyama.
An karbo Hadisi daga Sauban (R.A) ya ce: Manzon Allah (SAW) ya ce: “Lallai Allah Ya nade mun kasa har sai da na hango karshen gabashinta da karshen yammacinta. Kuma lallai al’ummata mulkinta zai kai har inda na hango. Kuma an ba ni taskoki biyu jajaye da farare (wato zinari da azurfa). Kuma lallai na roki Ubangijina game da al’ummata, cewa kada a halakar da ita da fari (yunwa), kuma kada a dora makiyansu su ci nasara a kansu. Kuma lallai sai Ubangijina Ya ce: “Ya kai Muhammad, lallai ka sani, idan na hukunta wani hukunci ba na mai da shi. Na yardar maka cewa al’ummarka ba za su halaka da yunwa ko fari ba, kuma na yardar maka koda dukkanin kafiran duniya gaba daya sun taru a kan al’ummarka ba za su yi galaba a kansu ba, har sai idan ya kasance sashinsu ne yake halaka sashi, sashinsu ne yake kama sashi a matsayin fursunan yaki.”
A ruwayar Abu Dawuda ya kara da cewa: “Sani cewa, kadai abin da nake ji wa al’ummata tsoro, su ne, jagorori (shugabanni) batattu. Sannan kuma da zarar al’ummata sun fara yakar juna, to, (Allah Ya kiyaye) ba zai dakata ba, zai ci gaba har tashin Alkiyama. Kuma Alkiyama ba za ta tsayu ba, har sai an samu a cikin al’ummata mutanen da za su hade da mushirikai suna ayyuka irin nasu. Kuma har sai an samu a cikin al’ummata, wasu kabilu sun koma bautar gumaka. Kuma da sannu zai kasance makaryata talatin sun bayyana a cikin al’ummata, kowannensu yana riya cewa shi Annabi ne. Ku sani ni ne Cikamakin Annabawa, babu wani Annabi da zai zo a bayana. Kuma wata jama’a ba za ta gushe ba daga al’ummata a kan gaskiya, suna taimakon (gaskiyar), duk wani da zai saba musu bai dame su ba. Suna nan a kan (gaskiyar) har al’amarin Allah Ya riske su a kan haka.” Muslim da Abu Dawuda da Tirmizi da Ahmad ne suka ruwaito.
An karbo Hadisi daga Mu’azu bin Jabal (R.A) ya ce: “Wata rana Annabi (SAW) ya yi wata Sallah mai tsawo (ya tsawaita ta), bayan ya kare, sai muka ce: “Ya Manzon Allah, yau ka tsawaita sallah. Sai ya amsa cewa: “Na yi Sallah ce da ke cike da kwadaitarwa da firgitarwa. Na roki Allah Ya yi min abubuwa uku game da al’ummata, sai Ya amince mani da guda biyu, Ya ki yarda da daya. Na roki Allah kada Ya dora makiyi a kan al’ummata daga waje, Ya yarda mani wannan. Na roki Allah kada Ya sa al’ummata su rika yakar junansu (suna kisan juna), amma Allah bai karbi wannan ba.”

Imam Murtada Muhammad Gusau
Babban Masallacin Juma’a na Nagazi Okene, Jihar Kogi
08038289761