Kashe Kwamred Bala Shugaban Cibiyar Horar da Naƙasassu ta Abuja ya ta da hankali

Marigayin shi ne shugaban cibiyar na farko kuma da ke ci gaba da jagoranci tun bayan kafa ta sama da shekara 20 ke nan a yanzu,

Kashe Kwamred Bala Shugaban Cibiyar Horar da Naƙasassu ta Abuja ya ta da hankali

Iyalai da sauran ’yan uwan Shugaban Cibiyar Horar da Naƙasassu ta Abuja, Kwamred Bala Tsoho Musa da aka yi wa kisan gilla, na ci gaba da bayyana alhini kan lamarin.

Kisan wanda ya auku a ranar Juma’a mako biyu da suka gabata da misalin ƙarfe 10 na dare. An kashe jagoran ne a ƙofar gidansa da ke cikin harabar cibiyar da ke ƙauyen Kuchiko, a bayan garin Bwari, Abuja, ta hanyar bugun sa da wani katako da ke wajen sannan a ka bar shi cikin jini a kusa da kekensa na guragu.

Marigayin shi ne shugaban cibiyar na farko kuma da ke ci gaba da jagoranci tun bayan kafa ta sama da shekara 20 ke nan a yanzu, a lokacin tsohon Ministan Birnin Tarayya, malam Nasir Ahmad Elrufa’i, aka samar da cibiyar don samar da horo kan sana’o’i ga mabarata da sauran al’umma da ake kamawa a birnin da ke yawon gararanba ko talla.

Malam Bala Tsoho Musa wanda ɗan asalin Ƙaramar Hukumar Bokkos ta Jihar Fulato ne, ya halarci makarantarsa ta firamare a yankin sai kuma Makarantar Horar da Malamai ta Zawan da ke Jos babban birnin Jihar Filato. Daga bisani ya wuce zuwa Jami’ar Jos, inda ya samu shaidar digiri na farko da kuma na biyu. Tuni dai a ka binne shi a kashegari bayan yi masa sallar jana’iza a fadar Sarkin Bwari, Alhaji Muhammad Auwal Ijakoro.

Ya rasu ya bar mahaifiyarsa da mata 3 da kuma ’ya’ya shida. A zantawarta da Aminiya, uwar gidan marigayin mai suna Lauratu Abdullahi ta ce, ta yi masa gani na ƙarshe da misalin ƙarfe 7 na dare a lokacin da ta koma ɗakinta kasancewar tana fama da zazzaɓi a ranar.

Ta ce “ya ci gaba da kasancewa tare da sauran abokan zamana biyu da kuma yara har zuwa bayan ƙarfe 9 na dare kafin ya fita kewaye a cikin cibiyar, sannan daga baya ya dawo barandar gidan don hutawa kamar yadda ya saba yi kafin ya kwanta barci.” Wata bebiya ce da ke zuwa nan gidan tana taya mu aiki daga cibiyar ta fara ankarar da mu lamarin, bayan ta fita daga wajenmu za ta koma makwancinta. Sai kawai mu ka jita ta na ta ƙwala ihu tare da yanayin kuka, a nan ne muka garzayo zuwa wajen.”

Ta ci gaba da cewa, ”abin ya tayar mana da hankali matuƙa ganin irin halin da muka same shi a ciki, saboda an illata masa kai sosai,” in ji ta

Ta yi addu’ar Allah Ya sa ƙarshen wahalar ke nan. Ita ma a zantawarta da Aminiya, matar marigayin ta biyu mai suna Bilkisu Haruna ta ce, ta fara sanin marigayin ne a Cibiyar Horar da Naƙassau ta birnin Jos, sannan bayan wasu ’yan shekaru sai suka yi aure.

Ta bayyana shi a matsayin mutum mai taimako ga al’umma tare da addu’ar Allah Ya gafarta masa kurakuransa.

Amaryar marigayin mai suna Zainab Muhammad ta ce, a watan Disamba mai zuwa ne za su cika shekara 3 da yin aure da Allah Ya albarkace su da samun ɗa guda. Ta ce marigayin ya yi wa ƙasarsa hidima bakin gwargwado sannan a ƙarshe ya rasa ransa a bakin aiki. “Ina kira ga gwamnati da ta saka masa ta hanyar kula da abin da ya bari,” in ji ta.

Wani ƙanin marigayin mai suna Ibrahim Tsoho Musa da shi ma ya ke da zama a kusa da garin na Bwari ya bayyana yadda labarin mutuwar ya je masa. ”Uwar gidansa ta buga mini waya ’yan mintuna kaɗan bayan ƙarfe goma, inda ta shaida mini mummunan abin da ya faru. A kan hanyata ta zuwa ne na yi kiciɓis da motar ’yan sanda da na kula da wani ɗan uwana da ke tare da su. A nan na juya da motata, na bi su zuwa Babban Asibitin Bwari, inda suka garzaya da shi don tantance shi, inda likitoci suka tabbatar da ya rasu.”

Da farko na buƙaci da mu koma da gawar gida tun a daren don fara yi mata shirin jana’iza, amma sai dai ’yan sanda ba su amince ba. Mun wuce da ita zuwa ɗakin adana gawa na wani asibitin coci da ke nan garin Bwari kasancewar babban asibitin garin bai da irin ɗakin,” in ji malam Ibrahim.

Ya ce, bayan nan sun koma cibiyar tare da ’yan sandan, inda suka fara gudanar da bincike ta hanyar zagaya ɗaukaci cibiyar, sannan daga bisani aka gayyaci ma’aikatan da ke aiki a daren da sauran masu kwana a wajen, in ban da ɗalibai.”

“Da farko an wuce da wasu ma’aikata uku da suka haɗa da limamin masallacin cibiyar kuma ɗaya daga cikin masu koyarwa mai suna Garba Idris, sai Bala Tanko shi ma maa’ikaci ne sai kuma wanda ke taimaka masa wajen tura shi a kan keke mai suna Abubakar Haruna. Gaba ɗayansu mutane ne da ke da dangantaka da mu. Sai dai an sake su a daren Talata bayan shafe yini uku a ofishin ’yan sanda na Bwari, inda aka tantance su.”

Ya ƙara da cewa, “akwai kuma ɗan sanda ɗaya da kuma jami’in tsaro na Sibil difensa da su ma aka wuce da su ofishin kafin a sake su a daren bayan, sun ba da bahasinsu.

Sai dai mutum na shida wani mai gadi da ya yi sa-in-sa da marigayi ɗan’uwan namu kamar yini biyu gabanin kisan, an ci gaba da tsare shi. Sun yi taƙaddamar ne kan dakatar da shi da ya yi a sakamakon sulalewar da wasu mutum biyu suka yi a baya, amma sai ya ce ba zai bar gidan ba har sai an biya shi ragowar albashinsa na wata biyu.”

Malam Ibrahim Tsoho ya ce, ’yan sanda sun sake komawa wajen a daren Talata, inda suka yi awon gaba da mutum biyu, namiji mai suna Linus da kuma mace mai suna Blessing wanda namijin ke kula da ɓangaren maza ita kuwa macen ke kula da mata da aka tsare a cibiyar. Mataimakin Jami’in Hulɗa da Jama’a na Rundunar ‘Yan sanda na Abuja, ASP Apeɓerga Patrick ya tabbatar da aukuwar lamarin ga wakilinmu ta waya a ranar Laraba, inda ya ce za a ci gaba da tsare mutane uku don faɗaɗa bincike a kansu.

Hajiya Fatima Idris ita ce mahaifiyar marigayin, wadda ke da zama a garin Jos. Bayan faruwar lamarin ta garzayo zuwa gidan kashegari ranar Asabar tare da sauran danginsa, inda suke karɓar gaisuwa. Ta bayyana wa Aminiya yadda ta rasa samun ɗan nata a farkon yinin ranar da ibtila’in ya auku da shi.

“Na kira shi kamar sau biyu a farkon yinin ranar ba tare da ya samu damar ɗaukar wayata ba. Can da daddare ne ya kira ni da misalin ƙarfe 9, inda yake ba ni haƙuri sannan da ya ji ina cikin yanayi na barci sai ya ce zai dakatar da wayar da nufin sake kira na washegari da safe.”

Ta ci gaba da cewa, “ashe ƙarshen maganata da shi ke nan. A yanzu na rasa mai taimaka mini da bai san babu ba, a duk buƙatar da na gabatar masa ta rayuwa,” in ji Hajiya.

A yayin rayuwarsa, Kwamred Bala Tsoho Musa wanda ya yi ƙaura zuwa birnin Abuja a dalilin rigimar farko da ta auku a garinsu na Jos. Ya fara ne da sana’ar walda a birnin kafin daga bisani aka ɗauke shi aikin koyarwa a cibiyar, inda ya haɗa da koyar da sana’ar tasa ga ɗaliba da ke da sha’awar aiki, kai-tsaye kamar yadda ɗaya daga cikin ’yan uwansa ya bayyana wa Aminiya.

Bayanai sun ce, marigayin yana taimaka wa ’yan’uwansa da dama wajen ɗaukar su aiki a cibiyar, wadda a farko ta yaye ɗalibai da dama tare da ƙarfafar su da jarin kayan aikin bayan an yaye su. Daga baya ne cibiyar ta rasa darajarta a dalilin rashin samun cikakkiyar kulawar gwamnatoci da suka biyo bayan shuɗewar minitsan da ya kafa ta.

Wasu da ke da nasaba da wajen sun yi zargin cewa, cibiyar ta koma tamkar wajen garƙame dukkan nau’ukan mutane da a ka kama daga cikin birnin Abuja ciki har da matasa masu ta’ammali da miyagun ƙwayoyi da kuma waɗanda iyayensu ke kai su wajen da kansu bayan sun zama kangararru.

Haka kuma an yi zargin cewa, matsalar karɓar na goro wajen ba da belin kamammu ya yi ƙamari a wajen, sai kuma amfani da cibiyar wajen kasafin kuɗi da ba a tantance yadda aka kasha shi ba da sunan tsabtace birnin Abuja.

 

Tsofaffin ma’aikatan Gombe 2,204 sun karɓi giratuti N4.2bn

Bam ya yi ajalin ɗaliban Islamiyya 2 a Abuja 

Mamakon ruwan sama ya haddasa ambaliya a Saudiyya

’Yan sanda sun ceto yara 4 da aka sace daga Bauchi a Anambra