… Kashe malamai alama ce ta saukar masifa – Ustaz Sambo Dukku

Shugaban Majalisar Malamai ta kungiyar Jama’atu Izalatil Bidi’a Wa Ikamatis Sunnahta Jihar Neja Malam Muhammad Sambo Dukku ya ce yawan kashe malamai da ake yi a kasar nan alama ce ta saukar masifa.Malam Muhammad Sambo ya bayyana haka ne a Minna yayin da yake amsa tambayoyin manema labarai game da kisar gillar da ’yan bindiga […]

… Kashe malamai alama ce ta saukar masifa – Ustaz Sambo Dukku
… Kashe malamai alama ce ta saukar masifa – Ustaz Sambo Dukku

Shugaban Majalisar Malamai ta kungiyar Jama’atu Izalatil Bidi’a Wa Ikamatis Sunnahta Jihar Neja Malam Muhammad Sambo Dukku ya ce yawan kashe malamai da ake yi a kasar nan alama ce ta saukar masifa.
Malam Muhammad Sambo ya bayyana haka ne a Minna yayin da yake amsa tambayoyin manema labarai game da kisar gillar da ’yan bindiga suka yi wa fitaccen malamin addinin Musuluncin nan da ke Zariya, Sheikh Muhammad Awwal Albani da wasu daga cikin iyalansa matarsa a makon jiya.
Shugaban ya nuna takaicinsa kan yadda irin wannan kisan gillar ya zama ruwan dare a nan Arewa, inda ya bayyana Sheikh Awwal Albani da malamin Sunnah na gaske da ya sadaukar da rayuwarsa wurin isar da sakon Musulunci bisa koyarwar Annabi Muhammad (SAW) da sahabbansa.
Ya yi kira ga Gwamnatin Tarayya da gwamnatocin jihohi da jama’a su rika bayar da gudunmawar da za ta taimaka domin shawo kan wannan matsalar da ta zama barazana ga addini da walwala da tattalin arziki.
Ya yi kira ga masu kiran kansu Ahlis Sunnah da suke yawon bin masu hannu da shuni da manyan ma’aikatan gwamnati da sunan neman taimakon gidauniyar marayu ko marasa galihu a madadin kungiyar Izala alhali ba a sa su ba, su ji tsoron Allah su bari. Ya shawarci masu sha’awar taimaka wa gidauniyar su ziyarci masallatan Ahlis Sunnah mafi kusa da su domin isar da sakon ga wadanda suka kamata.Ya ce hikimar bullo da shirin ita ce, a tallafa wa wadannan rukunan mutanen samun damar gudanar da rayuwa cikin sauki.
A karshe, ya gode wa Gwamnan Jihar Neja Dokta Mu’azu Babangida Aliyu kan cika wa kungiyar alkawarin samar mata motocin safa biyar, inda reshen jihar na kungiyar ya samar masa da daya domin gudanar da ayyukanta na wa’azi da da’awa.