Kashe malamai ba zai hana addini ci gaba ba (2)

Ya ku bayin Allah! Yaya labarin kisan gillar da aka yi wa wasu daga cikin iyalin Gidan Manzon Allah? Yaya kisan gillar da Hajjaj bin Yusuf As-Sakafi ya yi wa Sa’id bin Jubair (RH)? Shin yanzu mun manta da irin azabar da bayin Allah irin su Ahmad bin Hambal suka sha domin yada addinin Allah […]

Kashe malamai ba zai hana addini ci gaba ba (2)

Ya ku bayin Allah! Yaya labarin kisan gillar da aka yi wa wasu daga cikin iyalin Gidan Manzon Allah? Yaya kisan gillar da Hajjaj bin Yusuf As-Sakafi ya yi wa Sa’id bin Jubair (RH)? Shin yanzu mun manta da irin azabar da bayin Allah irin su Ahmad bin Hambal suka sha domin yada addinin Allah da karantar da al’umma?
Yaya batun babban malami Shahidi Abubakar bin An-Nabulusi (RH) ya kasance a lokacin jajircewarsa a kan tunkarar zalunci da azzalumai?  Wallahi ’yan uwa Musulmi masu girma, fede fatar jikinsa aka yi da ransa har sai da ya mutu! Yaya labarin babban malami Shehun Musulunci Ibnu Taimiyya Al-Harraniy (RH) ya kasance domin tunkarar zalunci da azzalunmai? Wannan bawan Allah ya kasance an daure shi ba iyaka, kai daga karshe ma makiya gaskiya sun daure shi a gidan yari a ciki ma Allah Ya karbi ransa!
Ya ku bayin Allah! A gaskiya da zan yi ta kawo mutanen da suka hadu da zaluncin azzalumai, makiya Allah, makiya gaskiya, wallahi sun kai dubbbai, amma don takaitawa zan bar su haka.
Kawai abin da yake muhimmi mu fahimta shi ne, wannan irin kisan gilla da aka yi wa Sheikh Muhammad Auwal Adam Albani, ya sha faruwa da bayin Allah mutanen kirki kafin shi. Amma wannan bai dakatar da ci gaban Musulunci ba, ko a nan kasar akwai abubuwa da dama da suka faru na kisan gillar da azzalumai suka yi wa wasu daga cikin bayin Allah, amma a karshe, sai ya zamar musu alheri. A kullum aka ambace su, za ka ji kamar yau aka yi su. Misali mutane irin su, Sa Ahmadu Bello, Sardaunan Sakkwato da Sa Abubakar Tafawa balewa, Firayi Ministan Najeriya da ma wanda ya faru kwanan nan, irin kisan gillar da aka yi wa babban malami Sheikh Ja’afar Mahmud Adam da Sheikh Umar dan Maishiyya Sakkwato da Malam Husaini Mayo-Belwa, wanda shi ina tsammanin ma yau sama da shekara 10 ko labarin gawarsa ba a samu ba.
Ya Allah muna rokonKa don tsarkin sunayenKa Ka tona asirin wadanda ke yi wa al’umma wannan ta’addanci, amin.
Huduba ta Biyu:
Bayan godiya da yabo ga Allah.
Ya ku Bayin Allah! Mu sani tafarkin da’awa da kira a kan gaskiya da yakar rashin gaskiya yana cike da matsaloli da wahalhalu iri-iri, kamar yadda Babban Malami Fadilatus-Sheikh Muhammad Hasan ya kawo a littafinsa mai suna: ‘Khawadir Ala darikid-Da’awa.’ Kama daga dauri da wulakanci da kisa da sauransu. ’Yan uwa Musulmi masu girma! Kawai mu zama masu dauriya da hakuri a kan abin da duk zai same mu a tafarkin da’awa. Kamar yadda Lukmanul Hakim ya yi wa’azi da nasiha zuwa ga dansa, cewa: “Ka yi umarni da kyakkyawan aiki, ka yi hani daga mummuna kuma ka yi hakuri da duk abinda zai same ka na cutarwa.”
Sannan insha-Allah, Sheikh Muhammad Auwal Adam Albani muna sa rai da fatar Allah (SWT) Ya karbi shahadarsa. Kuma Allah Ya sada shi da dukkan falalar da masu shahada suke samu. Kamar gafarar Allah da samun Aljanna da kubuta daga azabar kabari da aminci daga firgici babba da kambin sarauta na natsuwa da ceton da Allah zai ba shi na mutum saba’in daga danginsa da ’yan matan Aljanna na Hurul Ain.
Allah Ya haramta wa kasa cin jikin shahidi, Allah na matukar so da kaunar shahidai, shahidi aikinsa da ya aikata yana raye zai ci gaba da gudana (ladar) ba zai tsaya ba. Sannan matsayin shahidi ne kawai ya yi kusa da matsayin Annabawa. Jinin shahidi yana da daraja a wurin Allah, sannan shahidi ne kawai zai yi fatar ina ma a ce zai dawo duniya a sake kashe shi. Saboda irin abin da zai gani na sakamakon shahidai.
Sannan tun daga lokacin da jininsa na farko zai diga a kasa an gafarta zunubansa, kuma ba zai taba jin zafi da radadin ciwon harbi ko suka ko sararsa da aka yi a yayin kashe shi ba. Kai wallahi in takaice muku labari, falalar shahada tana da matukar yawan da ba zan iya kawo su duka a wannan Huduba tawa ba. Kuma insha-Allah muna fatar Sheikh Albani ya yi sa’a kuma tasa ta yi kyau. Makasansa kuma in sha Allahu ba su ba kwanciyar hankali. Domin Allah (SWT) Ya yi alkawarin daura yaki da duk wanda ke adawa da masoyanSa.
Domin karin bayani game da falalar shahada, ma’anar shahada da shahidai, a samu littafin Babban Malami Al-Imam Muhyiddin Abu Zakariyya Ahmad bin Ibrahim bin-Nuhaas Al-Dimashkiy Al-Dumyati, mai suna “Mashari’il Ashwak ila masari’il ush-shaak.” Da littafin Babban Malamin Hadisi na wannan zamani, Ash-Sheikh Muhammad Nasiruddeen Al-Albani, mai suna: “Ahkaamul Janaa’iz wa bida’uha.” Da kuma littafin Shehun Malami, Yusuf bin Daifillah Ash-Shabiliy, mai suna: “Iykaazu zawil-Himam bi ma’arifatu ma yanaluhush-shahidu minal fada’ili wal-karam.” Insha-Allah a cikin wadannan littattafai da sauransu, za a tarar da hujjoji yankakku da za su tabbatar da cewa lallai Baban Abdurrahman ya yi shahada bi’iznillah.
Sannan ya ku bayin Allah! Mu yi hakuri da abinda ya faru, mu dauki dangana. Sannan wannan al’amari kada mu taba yarda ya sare mana gwiwa, ya sa mana rauni, ya razana mu. Mu dauki wannan a matsayin wani abu da Allah (SWT) Ya kaddara. Domin na daga cikin ginshikan imani, imani da kaddara mai kyau da marar kyau. Mu dauki wannan al’amari a kan Allah (SWT) Ya kawo shi ne domin Ya karrama Sheikh Albani da shahada kuma Ya daukaka darajarsa.
Sannan game da almajiran Malam da sauran al’umma, ina kira a kan cewa lallai kada a bar karantarwar Malam ta tafi a banza, dukkan makarantunsa ya zama wajibi su ci gaba da gudana. Sannan a yi kokarin samun halifan Malam, wanda zai ci gaba da jagorantar al’amura. Kamar yadda bayan kisan gillar da aka yi wa Sheikh Ja’afar, komai ya ci gaba. Domin makiya su san cewa ita gaskiya wallahi babu mai iya dakatar da ci gabanta ta kowace hanya. Kuma su sani kokarin dakatar da ita bata lokaci ne kawai.
Ina mika ta’aziyya ta ga iyalan Malam da ’yan uwansa da dalibansa da masoyansa da aminansa da daukacin al’ummar Musulmin Najeriya a kan wannan babbar asara da Musulunci da Musulmi suka yi. Ina rokon Allah (SWT) Ya ba mu hakuri da juriya da dangana, amin.
Kuma ina mika sakon ta’aziyya zuwa ga babban amini daga cikin aminan Malam, wato Sheikh Sa’id Aliyu Maikwano Gusau, Allah Ya ba mu hakuri dukkanmu, amin.
Sannan ina kira ga malamai da almajirai da kada kisan malami ya sanya su razana, su ji tsoron fadar gaskiya da bayyana wa al’umma hakikanin me ke faruwa. Su sani cewa a lokacin da Allah Ya halicci kowanenmu ya rubuta abincinsa da ajalinsa da abin da zai same shi da sauransu. Kuma su sani ita mutuwa lallai kowane mutum sai ya dandane ta. Ko an kashe ka ko ba a kashe ka ba, za ka mutu. Allah (SWT) Ya ba mu labari cewa, lallai ba a jinkirta wa rai idan ajalinta ya zo. Sannan lokacin da Allah Ya rubuta kowa zai mutu, to lokacin na yi zai mutu. Babu karin lokaci babu ragi.
Ya ku bayin Allah! Yaya labarin kisan gillar da aka yi wa wasu daga cikin iyalin Gidan Manzon Allah? Yaya kisan gillar da Hajjaj bin Yusuf As-Sakafi ya yi wa Sa’id bin Jubair (RH)? Ya Allah muna rokonKa don tsarkin sunayenKa Ka tona asirin wadanda ke yi wa al’umma wannan ta’addanci, amin.
Imam Murtada Muhammad Gusau
08038289761