Kashe malaman addini da kama-karya ta sa muka bar PDP – Tsohon Shugaba

  Daga Tsohon Shugaban Jam’iyyar PDP na Sakkwato ta Arewa kuma shugaban kungiyar shugabannin jam’iyyar na Jihar Sakkwato Alhaji Muhammad dangwaggo ya ce sun bar PDP ne zuwa APC saboda kashe malaman addini da kama karya da jam’iyyar ke yi a kasar nan, inda ta kasa magance rikicin Yobe da Adamawa da Borno.Shugaban ya fadi […]

Kashe malaman addini da kama-karya ta sa muka bar PDP – Tsohon Shugaba
Kashe malaman addini da kama-karya ta sa muka bar PDP – Tsohon Shugaba

 

Daga

Tsohon Shugaban Jam’iyyar PDP na Sakkwato ta Arewa kuma shugaban kungiyar shugabannin jam’iyyar na Jihar Sakkwato Alhaji Muhammad dangwaggo ya ce sun bar PDP ne zuwa APC saboda kashe malaman addini da kama karya da jam’iyyar ke yi a kasar nan, inda ta kasa magance rikicin Yobe da Adamawa da Borno.
Shugaban ya fadi wadannan kalamai ne a zantawar da Aminiya ta yi da shi a Sakkwato, inda ya ce “In babu lalura ta ci baya da tsohuwar jam’iyyarmu ke kawo wa al’umma da ba za mu bar ta ba, amma tunda ci gaba muke so dole mu nemi canji don wahalar ta isa, don haka muka shiga jam’iyya mai zaman lafiya da son ci gaba wato APC kuma duk dan kasa na kwarai ya san haka.”
Ya ce idan aka dubi Jam’iyyar APC a Jihar Sakkwato ita ke da nasara da yarda Allah “domin duk shugabaninmu na mulki da jam’iyya ba wani mutum da ya tsaya can a PDP, muna tare da mutanenmu, masu fadin za su kwata da karfi maganar banza ce don Allah ke ba da mulki,” inji dangwaggo.
Da tsohon shugaban ya juya kan ficewar Bafarawa daga jam’iyyar zuwa PDP, ya ce taimako ne na Allah da Ya yi masu don inda har yanzu Bafarawa na tare da su da ci gaban da aka samu bai zo ba, “Amma da ya koma inda yake samun kudi, nasarori kawai muke samu a tafiyarmu, fitar Bafarawa ba abin da ya rage ko kamar allura ta debo ruwa a gulbi,” inji shi.
Ya yi kira ga ’ya’yan jam’iyyar su zauna lafiya kada su yi siyasar tashin hankali kuma duk shirin da ya kamata a yi na samun nasarar APC an yi shi.