Kashe mana jami’ai ba zai kashe gwiwarmu wajen gudanar da aiki ba – Kwamishina

Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar Gombe Abdullahi Kudu Nma, ya ce kashe musu jami’ai da ‘’yan bindiga ke yi ba zai kashe musu gwiwa wajen gudanar da aikinsu na tabbatar da tsaron rayuka da dukiar jama’a ba, inda ya ce sun samu nasarori masu yawa a shekara biyu da suka gabata.Abdullahi Kudu Nma, ya bayyana haka […]

Kashe mana jami’ai ba zai kashe gwiwarmu wajen gudanar da aiki ba – Kwamishina

Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar Gombe Abdullahi Kudu Nma, ya ce kashe musu jami’ai da ‘’yan bindiga ke yi ba zai kashe musu gwiwa wajen gudanar da aikinsu na tabbatar da tsaron rayuka da dukiar jama’a ba, inda ya ce sun samu nasarori masu yawa a shekara biyu da suka gabata.
Abdullahi Kudu Nma, ya bayyana haka ne a lokacin da ya kira taron ’yan jarida a ofishinsa don bitar nasarori da kalubalen da suka samu a shekarun da kuma yadda za su fuskanci wannan shekara ta 2014.
A cewar Kwamishinan a bara 2013, sun samu nasarar kama ’yan fashi da makami 53 sun kuma gano bindigogin da suke amfani da su guda 34 da alburusai 1,101 da gidan makunsan harsashi 21.
Kwamishina Kudu Nma, ya kara da cewa sun kuma gano motoci 17 da barayi suka sace daga jama’a kuma sun kama masu yi wa yara fyade da dama a sassan jihar.
Kwamishinan ‘Yan sandan ya yi kira ga jama’ar jihar su rika ba su labaran da za su taimaka musu su samu nasara ya ce idan mutum yana tsoro ba sai ya je wurin kananan ’yan sanda ba, kofarsa a bude take su zo wurinsa kai-tsaye zai rufa wa duk wanda ya ba shi labari asiri.
Ya gode wa Gwamnan Jihar Gombe Alhaji Ibrahim Hassan dankwambo kan yadda yake b asu hadin kai da goyon baya wajen gudanar da aikinsu.