Kashe matashi ya kusa jawo rikici a Bauchi
Daba wa wani matashi dan shekara 18 mai suna Dindara Yusuf wuka a kirji, ya mutu a hanyar Bauchi zuwa Dass ya kusa jawo rikici a Bauchi. Kakakin ’Yan sandan Jihar Bauchi, DSP Kamal Datti Abubakar wanda ya tabbatar da aukuwar lamarin, ya ce ’yan sanda suna bincike har ma sun kama mutum bakwai, inda […]

Daba wa wani matashi dan shekara 18 mai suna Dindara Yusuf wuka a kirji, ya mutu a hanyar Bauchi zuwa Dass ya kusa jawo rikici a Bauchi.
Kakakin ’Yan sandan Jihar Bauchi, DSP Kamal Datti Abubakar wanda ya tabbatar da aukuwar lamarin, ya ce ’yan sanda suna bincike har ma sun kama mutum bakwai, inda yanzu haka suke sashen binciken manyan laifuffuka na ’yan sanda, ana bincikensu kuma da zarar an kammala bincike za a dauki mataki na gaba da ya dace da doka.
Kamal Datti ya ce an kashe matashin ne a ranar Asabar da ta gabata, kuma da aka zo binne gawarsa ce sai wadansu mutane suka ta da yamutsi a kauyen Yalwa.
Ya ce jami’an tsaro sun shawo kan lamarin kuma ba su kama kowa ba kan yamutsin.
Kakakin ya gargadi jama’a su guji ta da hayaniya ta hanyar daukar doka a hannunsu. Ya ce ’yan sanda za su tabbatar da an yi adalci kan wannan lamari.
Wadansu daga cikin mazauna Unguwar Yalwa sun ce kashe matashin ya biyo bayan musu ne da rashin jituwa da suka samu da wasu a lokacin da suka yi wani biki, kuma wadanda suka kashe shi sun biyo shi har inda suka same shi suka daba masa wuka a kirjinsa, suka yi kac-kaca da kirjin. Bayan an kai shi asibiti ne, sai ya mutu.
Mazauna Unguwar Yalwa da ke Bauchi sun bayyana cewa an sassari wadansu mutane da wuka, a lokacin hatsaniyar.