Kashe-Mu-Raba: Ana Binciken Tsohon Shugaban Mexico
Ana kuma zargin tsohon shugaban da halasta kudin haram da kashe-mu-raba da kamfanonin da ya ba kwangila a mulkinsa
Gwamnatin Mexicio ta kaddamar da bincike kan tsoho shugaban kasar, Pena Nieto, bisa zargin almundahana da halasta kudaden haram.
Binciken ya taso ne bayan hukumar yaki da rashawa ta kasar ta zarge shi da karkatar da wasu miliyoyin daloli da ta ce na haramun ne.
- Za mu kori duk wani azzalumin alkalin kotun Musulunci —Gwamnatin Borno
- Kamfanonin hada motoci 52 sun durkushe a Najeriya
Ofishin Babban Mai Gabatar da Kara ta Kasar ya fitar, ta ce zarge-zargen na da alaka da zabe.
Amma kuma ta bangaren azurta kai ana zargin sa da aikewa da kuma karkatar da kudade da kuma alaka da wani kamfanin gine-gine na kasar Spain.
A watan Yuli ne hukumar ta ce tsohon shugaban ya karbi kimanin Dala Miliyan1 1.25 daga wani dan uwansa a Mexico.
Hakan ta sa hukumar ta binciki ire-iren wadannan kudaden da ake aiko masa da ba a san asalinsu ba.
Ana zargin alakarsu da kamfanonin da ya ba kwangiloli masu tsoka a lokacin da yake shugaban kasa a shekarun 2012 zuwa 2018.
Tsohon shugaban ya musanta zargin.