‘Kashi 20 na mutanen Afirka ta Kudu suna dauke da Coronavirus’
Ministan Lafiya na kasar Afirka ta Kudu, Dokta Zweli Mkhize ya ce sabon bincike ya kiyasta cewa mutum miliyan 12 – kimanin kashi 20 na daukacin al’ummar kasar – watakila suna dauke da cutar Coronavirus. Wannan adadin ya dara yawan mutanen da kawo yanzu a hukumance aka tabbatar sun kamu da cutar a kasar na […]
Ministan Lafiya na kasar Afirka ta Kudu, Dokta Zweli Mkhize ya ce sabon bincike ya kiyasta cewa mutum miliyan 12 – kimanin kashi 20 na daukacin al’ummar kasar – watakila suna dauke da cutar Coronavirus.
Wannan adadin ya dara yawan mutanen da kawo yanzu a hukumance aka tabbatar sun kamu da cutar a kasar na fiye da mutum dubu 650 nesa ba kusa ba.
- COVID-19 ta mayar da ci gaban duniya baya da shekara 20 –Bill Gates
- Jami’an lafiya 41,000 sun harbu da COVID-19 a Afirka —WHO
“Nazarin ya dogara ne da binciken kwayoyin halittar garkuwar jiki da ke yawo a jinin marasa lafiya,” inji Ministan.
Cikin wani jawabi da aka fitar ranar Litinin ta makon da ya gabata, Dokta Mkhize ya ce raguwar alkaluman masu kamuwa da cutar ya haifar da ayar tambaya kan yaya karfin garkuwar jiki daga kamuwa da cututtuka yake a kasar.
Ya ce samfurin nazarin na farko ya nuna adadin kwayoyin garkuwar jikin tsakanin “kashi 29 zuwa 40” a cikin jinin mutane.
“A halin yanzu dai za a gudanar da bincike kan adadin kwayoyin halitta na garkuwar jiki na jama’ar kasar baki daya,” inji shi.
Sakamakon wani nazari kwatankwacin wannan da aka gudanar a Birtaniya da aka wallafa a watan Agusta ya gano cewa kashi 6 na mutane suna da garkuwa daga kamuwa da cutar Coronavirus.
“Sai dai lamarin ya fi karfi a birnin Landan inda kason ya kai 13 cikin 100.”
“Sai dai babu karin haske kan tsawon wane lokaci garkuwa daga cutar za ta ci gaba da wanzuwa a jikin mutane, ko kuma kamuwa da cutar a karon farko na nuni da cewa mutum ya samu garkuwar ba zai sake kamuwa da ita ba a karo na biyu,” inji shi.