Kashi 25 cikin 100 na ma’aikatan NAHCON sun hakura da aikin Hajji don hidima ga alhazai
Kimanin kashi 25 cikin 100 na ma’aikatan Hukumar Hajji ta kasa (NAHCON) da suka hada da ko’odinetocin shiyya da masu kula da tashi da karbar alhazai a cibiyoyin aikin Hajji sun amince su hakura da yin aikin Hajjin bana domin yin hidima ga alhazan Najeriya da kuma kula da harkokin Hajji domin ganin an gudanar […]
Kimanin kashi 25 cikin 100 na ma’aikatan Hukumar Hajji ta kasa (NAHCON) da suka hada da ko’odinetocin shiyya da masu kula da tashi da karbar alhazai a cibiyoyin aikin Hajji sun amince su hakura da yin aikin Hajjin bana domin yin hidima ga alhazan Najeriya da kuma kula da harkokin Hajji domin ganin an gudanar da ingantaccen aikin Hajji a bana.
Ma’aikatan da suka sadaukar da kansu don yi wa alhazai hidima a masallatai masu alfarma ba tare da shiga Ihrami ba sun ce su yi haka ne don koyi da Shugaban Hukumar, Barista Abdullahi Mukhtar Muhammad wanda ya hakura da aikin Hajji don gudanar da hidima ga alhazan Najeriya. Sun amince cewa kasancewa cikin Ihrami zai iya kawo musu cika wajen bayar da kyakkyawar kula ga alhazan.
A tattaunawa daban-daban da aka yi da su a Makkah ko’odinetocin shiyyar Sakkwato da Kano, Alhaji Abubakar Bello Kaoje da Umar Bala, sun ce sun yi farin ciki da tsarin hukumar saboda ta dalilin alhazai suka zuwa Saudiyya. “daukacin ko’odinetocin shiyyar sun yarda su hada karfi wajen gudanar da wannan ingantaccen tsari. Mun zo nan ne saboda alhazai kuma nauyin da aka dora mana shi ne mu tabbatar sun samu kyakkyawar kulawa bisa la’akari da kimar kudin da suka biya. Abin farin ciki ne gare mu yin hidima ga alhazai saboda Allah,” inji Kaoje.
“Bayan haka fifita lamarin alhazanmu ne a kan gaba. Sai kuma sauran al’amura su biyo baya. Wannan shi ne dalilin da ya sanya daukacin masu jan ragamar sassa muka yarda mu tallafa wa tsarin sa-kai. Kodayake sauran ma’aikata sun saba da aiki, sai dai wannan tsarin ya jawo karin ma’aikata sun shigo ciki. Wannan mataki ne mai kyau da hukumar ta dauka,” inji Bala, inda ya ce sakamakon da ake sa ran samu kyakkyawa ne, kuma zai haifar da cikakkiyar nasara a wannan aiki na Hajjin mashahuran wuraren ibada masu alfarma.
Wadansu ma’aikata da aka tattauna da su, sun nuna farin cikinsu da wannan sabon tsari. Sun yi farin ciki jin cewa tsarin zai rika jujjuyawa, ta yadda wadanda suka yi aikin sa-kai a bana, za su yin aikin Hajji a badi.
Idan za a tuna a lokacin aikin Hajjin bara, Shugaban Hukumar NAHCON da wadansu kalilan ma’aikata ba su yi aikin Hajji ba, inda hakan ya samar da gagarumar nasara. Don haka taron masu ruwa-da-tsaki da aka yi a Abuja ya amince a taron masu ruwa da tsarin a matakin kasa da jihohi. Kuma hakan ya sa NAHCON ta bukaci ma’aikatanta su yi aikin sa-kai, kuma sun amsa kiran sosai.