Kashi 25 cikin dari na matasan yammacin Afirka na dauke da HIb
Majalisar dinkin Duniya ta ce, an samu karuwa a yawan matasa da ke mutuwa sakamakon kamuwa da cutar HIb a kasashen da ke yammaci da kuma tsakiyar Afirka. A cikin wani sabon rahoto da UNICEF da kuma UNAIDS suka fitar sun ce, a cikin yara biyar da ke dauke da kwayar cutar HIb, hudu daga […]

Majalisar dinkin Duniya ta ce, an samu karuwa a yawan matasa da ke mutuwa sakamakon kamuwa da cutar HIb a kasashen da ke yammaci da kuma tsakiyar Afirka.
A cikin wani sabon rahoto da UNICEF da kuma UNAIDS suka fitar sun ce, a cikin yara biyar da ke dauke da kwayar cutar HIb, hudu daga cikinsu basa samun maganin da ke rage yawan radadin cutar.
BBC ta ruwaito Majalisar dinkin Duniyar na cewa kasashen da ke yammaci da kuma Tsakiyar Afirka su ne a baya a yakin da ake yi da cutar HIb/AIDS wajan samar wa yara da kuma manya magungunan da ke rage radadin cutar.
Shugaban asusun kula da yara ya ce yanayin da ake ciki abin takaici ne.
Kashi 25 cikin dari na yara da ke yankin na dauke da cutar HIb.
Rahoton na UNICEF da kuma UNAIDS ya ce, kasashe da dama a Afirka basu da isassun kayan aiki da ake bukata wajen yi wa jarirai gwaji.
Haka kuma matasa da ke yankin na cikin mawuyacin hali.
Yawan mutanen da suka rasu sakamakon kamuwa da cutar HIb ya karu da kashi 35 daga shekarar 2010 zuwa shekarar 2016 a tsakanin matasa masu shekara 15-19.
Majalisar dinkin Duniya ta ce yayin da yawan matasa zai karu a kasashe irinsu Jamhuriyar Dimukradiyar Congo da kuma Najeriya, za a ci gaba da samun karuwa a yawan mutanen da ke kamuwa da kuma mutuwa daga cutar HIb.