Kashi 63 na abun wanke hannu a Abuja jabu ne
Bincike ya gano cewa kashi 63 cikin 100 na man wanke hannu da ake amfani da shi Abuja mara inganci ne, kamar yadda rahoton cibiyar binciken hada magunguna ta Najeriya (NIPRP) kan yawaitar kayan jabu a kasuwanni ya tabbatar. Sakataren Gwamnatin Tarayya Boss Mustapha ya ce yawancin man wanke hannun masu dauke da sunadarin alkohol […]
Bincike ya gano cewa kashi 63 cikin 100 na man wanke hannu da ake amfani da shi Abuja mara inganci ne, kamar yadda rahoton cibiyar binciken hada magunguna ta Najeriya (NIPRP) kan yawaitar kayan jabu a kasuwanni ya tabbatar.
Sakataren Gwamnatin Tarayya Boss Mustapha ya ce yawancin man wanke hannun masu dauke da sunadarin alkohol ba su samu tantancewa ba daga hukumar NAFDAC mai kula da inganci abinci da magunguna.
A cewarsa, sakamakon binciken na Abuja, Babban Birnin Tarayya, alama ce ta halin da sauran sassan Najeriya ke ciki, don haka ya shawarci masu yin sunadaran da “su nuna kishin kasa su guji yin jabun kaya wadanda za su iya jefa ’yan Najeriya da ke saye a cikin hadari”.
Boss Mustapha wanda ke jagorantar kwamitin yakar cutar corornavirus da Shugaban Kasa ya kafa ya kuma yi kira ga ’yan Najeriya su guji amfani da man wanke hannu mai alkohol marasa lambar tantancewa na NAFDAC.