Kashi 63 na ’yan Najeriya ba su samun wadataccen abinci saboda talauci — NBS

Hukumar ƙididdiga ta Najeriya NBS ta ce wani bincike da ta gudanar ya gano cewa kashi 63.8 cikin 100 na gidajen ƙasar na cin abinci ɗan kaɗan saboda rashin kuɗi. Haka kuma NBS ta ce kashi 62.4 na gidajen na cikin fargabar rashin samun wadataccen abinci, sannan kuma kashi 60.5 cikin 100 na gidajen ba […]

Kashi 63 na ’yan Najeriya ba su samun wadataccen abinci saboda talauci — NBS

Hukumar ƙididdiga ta Najeriya NBS ta ce wani bincike da ta gudanar ya gano cewa kashi 63.8 cikin 100 na gidajen ƙasar na cin abinci ɗan kaɗan saboda rashin kuɗi.

Haka kuma NBS ta ce kashi 62.4 na gidajen na cikin fargabar rashin samun wadataccen abinci, sannan kuma kashi 60.5 cikin 100 na gidajen ba sa iya cin abincin da ya kamata a ce suna ci.

Binciken da hukumar ta gudanar ya mayar da hankali ne kan ƙaruwar talauci a tsakanin gidajen ƙasar da irin tasirin da hakan ke yi wajen raguwar sayen abubuwa da ’yan ƙasar suka yi sakamakon tashin farashinsu.

“Kusan kashi biyu cikin uku na gidajen Najeriya ba su iya cin lafiyayyen abinci mai ɗauke da sinadarai ko su dafa abinci saboda rashin wadata da suke fama da shi,” kamar yadda rahoton binciken ya nuna.

Haka kuma binciken ya gano cewa kashi rashin wadata ya sa kashi biyu cikin uku na gidaje a Najeriya ba su iya samun lafiyayyen abinci mai ɗauke da ingantattun sinadarai.

Rahoton binciken na zuwa ne ƙasa da wata guda bayan da wani rahoto da gwamnatin Najeriya ta fitar tare da tallafin Majalisar Ɗinkin Duniya ya nuna cewa ’yan ƙasar fiye da miliyan 33 za su fuskanci matsalar ƙarancin abinci a 2025.