Kashi 70 na dalibai ne suka fadi jarrabawar shiga makarantun gaba da sakandare a bana

A cikin  kashi  100  na daliban da  suka  zauna  jarrabawar  shiga  makarantun gaba da  sakandare, an bayyana cewa kashi 70 ne suka fadi wannan jarrabawar, musamman  ma  idan aka kwatanta  shi  da  yawan wadanda  ba su ci  jarrabawar  Turanci da lissafi ba.Da yake wa taron manema labarai bayani a birnin Ikko, shugaban hukumar jarrabawa ta […]

Kashi 70 na dalibai ne suka fadi jarrabawar shiga makarantun gaba da sakandare a bana
Kashi 70 na dalibai ne suka fadi jarrabawar shiga makarantun gaba da sakandare a bana

A cikin  kashi  100  na daliban da  suka  zauna  jarrabawar  shiga  makarantun gaba da  sakandare, an bayyana cewa kashi 70 ne suka fadi wannan jarrabawar, musamman  ma  idan aka kwatanta  shi  da  yawan wadanda  ba su ci  jarrabawar  Turanci da lissafi ba.
Da yake wa taron manema labarai bayani a birnin Ikko, shugaban hukumar jarrabawa ta kasasashen yammacin Afirka, Mista Charles Egurida ya ce  a wannan shekarar, daliban da  yawansu ya kai kusan dubu dari 3 ne suka zauna wannan jarabawar,  amma  wadanda  suka yi  nasarar samun  abin da  ake  bukata  a  matakin farko  na  shiga  makarantun  gaba  da  sakandare, su dubu 160 da ’yan kai ne, wadanda su ma  din ba lissafi da Turanci.
Ya ce  idan aka hada da wadanda  suka  samu Turanci da lissafi, yawansu bai haura dubu 86 ba, lamarin da ya nuna  ke nan kashi  29 da  digo 17, wanda ya yi daidai da kashi 70  da  digo 83  ke nan  suka  fadi  warwas.
Mista  Eguridu  ya ce idan aka kwatanta  faduwar  wannan shekarar  da  shekaru  biyu da   suka  gabata,  sai  a ga cewa  na  wannan shekarar ya fi muni  domin ko a  shekarar 2011 daliban da  yawansu  ya kai  kashi 36 da digo 7; kana  a  shekarar  2012 an sami kashi 37 da digo 97  suka  samu  nasarar  cin jarrabawan  ciki  ko  har da  lissafi da  Turanci, wadanda  su ne  kashin bayan jarrabawan  da  kuma samun damar  shiga  makarantun gaba da  sakandare.
Sai dai Mista Eguridu ya ce akwai jarrabawar daliba da aka  rike,  biyo  bayan samunsu da  magudi daban-daban kuma hukumar  tana  da kwamiti mai duba wannan, ta dauki  matakin da ya dace  kafin ta sanar  da makarantun daliban.
Shugabam hukumar  jarabawan ya ce  a  bisa  binciken da  suka  gudanar na dalilan da ke sa dalibai na  yawan  faduwa  jarabawa, shi ne wasu daga  cikin su  sun hada  da  rashin baiwa  fannin ilmi  fifikon da ya  dace  daga  gwamnati,  musamman abin da ya shafi  kudi,  sai kuma  rashin wadatattun  kayan aikin koyarwa, kana  iyaye  suna  nuna  halin ko-oho  ga  ilimin ’ya’yansu.
Ya ce  bai yiwuwa  a ce  a bar  malamai  da  kashin mahaukacin  kare.