Kashi 70 na ’yan Najeriya na amfani da maganin gargajiya —NNMDA
NAFDAC ta amince da wasu magungunan gargajiya biyar da aka yi bincike a kansu.
Cibiyar Bunkasa Magungunan Gargajiya ta Kasa (NNMDA), ta ce har yanzu kashi 70 cikin 100 na ’yan Najeriya na amfani da maganin gargajiya.
Darakta-Janar na NNMDA, Dokta Samuel Etatuvie, shi ne ya bayyana haka yayin zantawarsu da Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) a Abuja.
- Sau 66 muna dakile yunkurin yi wa taron Majalisar Zartarwa kutse —Pantami
- ’Yan Majalisar Kebbi 6 sun yi murabus
“A Najeriya, ina iya cewa kusan sama da kashi 70 na ’yan kasar na amfani da maganin gargajiya saboda karancin dakunan shan magani na zamani a karkara,” in ji Etatuvie.
A cewarsa, daga cikin magunguna 14 da suka yi bincike a kai, Hukumar Kula da Ingancin Abinci da Magunguna ta Kasa (NAFDAC) ta amince da guda biyar sauran kuma na kan hanya.
“Amfani da maganin gargajiya hanya ce dadaddiya, bayan shekaru da dama aka fara amfani da magungunan zamani.
“Yau a Najeriya da sauran kasashen duniya ana amfani da magani gargajiya da na zamani,” in ji shi.
Ya ce baya ga samar da lafiya, maganin gargajiya na da amfani ta hanyoyi da dama da suka hada da bayar da kariya da sauransu.
Ya kara da cewa, cibiyar na kokarin zurfafa bincike kan magungunan gargajiya wanda ke da karfin ba da gudunmawa ga ci gaban tattalin arzikin kasa.
(NAN)