‘Kashi 86 na ’yan Najeriya suna sayen fetur kan Naira 199 kowace lita’

Wani binciken jin ra’ayoyin jama’a da aka gudanar na “NOI Poll” ya ce kasha 86 cikin 100 na ’yan Najeriya suna sayen man fetur kan akalla Naira 199 kan kowce lita. Kamfanin da ya gudanar da binciken ya bayyana cewa a rahoton kwanan nan da suka fitatr a Abuja ranar Talatar da ta gabata ya […]

‘Kashi 86 na ’yan Najeriya suna sayen fetur kan Naira 199 kowace lita’

Wani binciken jin ra’ayoyin jama’a da aka gudanar na “NOI Poll” ya ce kasha 86 cikin 100 na ’yan Najeriya suna sayen man fetur kan akalla Naira 199 kan kowce lita.

Kamfanin da ya gudanar da binciken ya bayyana cewa a rahoton kwanan nan da suka fitatr a Abuja ranar Talatar da ta gabata ya tabbatar da cewa kudin litar man fetur ya yi matukar zarta Naira 145 kan kowace lita da Gwmanatin Tarayya ta kayyade.

Binciken wanda hadin gwiwa ne da hukumar kididdiga ta kasa (NBS) ya gano cewa rahoton sa’ido kan farashin man fetur ya yi nuni kan yadda ’yan Najeriya ke sayar fetur kan akalla Naira 191 kan kowace lita a Janairun bana.

Kamfanin y ace sakamakon binciken jin ra’ayoyin jama’ar, wanda aka gudanar ranar 5 ga Fabarairun bana, ya yi nuni kan muhimmancin bukatar ganin masu ruwka da tsaki a hada-hadar man fetur da iskar gas, musamman hukumar kula da albarkatun man ta DPR za ta kara kaimi wajen sa’ido kan yadda ake kayyade farashi.

’Yan bindiga sun kashe ’yan banga sun sace mai unguwa a Kaduna

A wata 19 Tinubu ya ciyo bashin tiriliyan 50

Jami’an Sibil Difens sun kashe mayaƙan Boko Haram 50

Sojoji sun kashe ’yan Boko Haram 30 a Borno