Kashi 90 cikin 100 na gwamnoni ba su cancanci shugabanci ba

Dokta Hakeem Baba-Ahmed ya ce a cikin kowadanne gwamnoni 10 mutum tara, “Ba su da shiri, ba su da kwarewa kuma ba su cancanci shugabanci ba”

Kashi 90 cikin 100 na gwamnoni ba su cancanci shugabanci ba

Kakakin Kungiyar Dattawan Arewa Hakeem Baba-Ahmed

Mai Magana da Yawun Kungiyar Dattawan Arewa (NEF), Dokta Hakeem Baba-Ahmed, ya ce kashi 90 cikin 100 na gwamnonin Najeriya ba su cancanci ko da samun kusanci da shugabanci ba.

Dokta Hakeem Baba-Ahmed ya kara da cewa a cikin kowadanne gwamnoni 10 a Najeriya, mutum tara, “Ba su da shiri, ba su da kwarewa kuma ba su cancanci shugabanci ba.”

Ya bayyana haka ne a lokacin da yake jawabi a Babban Taron Tattaunawa na Daily Trust na Shekara-shekara karo na 19 a Abuja, ranar Alhamis.

Baba-Ahmed ya ce a halin yanzu, mutanen da ba su dace ba ne suke jagorantar mutane suke musu karfa-karfa, su kuma mutanen suke ta neman samun sabbin shugabannin da suka dace, wanda shi ma bai wadatar ba.

Don haka ya yi kira da a sauya fasalin tsarin Najeriya, yana mai cewa, “Abin da ya kamata shi ne mu dora tsarin federaliyya da muke bi a kan gadon fida mu tambayi kanmu, ina matsalar take?

“Me ya hana a rage karfin shugabanci ko gudanar da shi, a sauya tsarin kasa, amma na san wannan batu ne da shugabannin yanzu suke yawan amfani da ita.