‘Kashi 90 na hadduran da suke aukuwa laifin mutane ne’

Babban Jami’in Kula da Ababen Hawa (bIO), na Jihar Zamfara Alhaji Aliyu Muhammad Zurmi ya ce kashi 90 cikin 100 na hadduran da ake samu a kasar nan, musamman a manyan hayoyi laifin masu amfani da ababen hawa ne da masu amfani da hanyoyin. Alhaji Aliyu Zurmi ya bayyana haka ne a wurin taron kungiyar […]

‘Kashi 90 na hadduran da suke aukuwa laifin mutane ne’
‘Kashi 90 na hadduran da suke aukuwa laifin mutane ne’

Babban Jami’in Kula da Ababen Hawa (bIO), na Jihar Zamfara Alhaji Aliyu Muhammad Zurmi ya ce kashi 90 cikin 100 na hadduran da ake samu a kasar nan, musamman a manyan hayoyi laifin masu amfani da ababen hawa ne da masu amfani da hanyoyin.

Alhaji Aliyu Zurmi ya bayyana haka ne a wurin taron kungiyar direbobin tanka na shiyyar jihohin Sakkwato da Kebbi da Zamfara da aka gudanar a garin Gusau a ranar Asabar da ta gabata.
Sai ya nemi direbobin tanka su rika tausayawa ’yan uwansu masu amfani da hanyoyi musamman masu kananan motoci, ya ce a wasu lokuta masu manyan motoci suna daukar kananan motoci kamar kwadi idan sun gamu da su a kan hanya, kamar yadda wasu daga cikinsu suke kiransu.
Ya kuma nemi manyan direbobin su rika lura da inda za su rika ba yaransu tuki, kuma su kauce wa neman ba su lasisin tuki na jabu tare da tabbatar suna nuna musu ka’idojin hanya don kauce wa haddura.
Alhaji Aliyu Zurmi ya ce Gwamnatin Tarayya ta tashi haikan wajen sanya alamomin hanya, musamman wuraren da suke miyagu ga direbobi, don samun saukin aukuwar hadari.
Shugaban ya jinjina wa shugabannin kungiyar ta direbobin tankar da suka hada taron, ya ce ta wannan hanyar za su samu dama fadakar da direbobi ka’idojin hanya da yadda ya kamata su rika tuki musamman m a irin wannan lokaci da rayuka suke yawan salwanta ta hadarin mota.