Kashi 90 na mutanen da Boko Haram ta kashe Musulmai ne – Buhari

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya bayyana cewa akasarin mutanen da mayakan Boko Haram suka kashe Musulmi ne, yana mai cewa burin ’ya’yan kungiyar shi ne su yi amfani da addini wajen raba kan ’yan Najeriya. A wata makala da BBC ta kalato daga daga jaridar Christianity Today, Shugaba Buhari ya ce bai kamata a kyale […]

Kashi 90 na mutanen da Boko Haram ta kashe Musulmai ne – Buhari

Shugaba Muhammadu Buhari

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya bayyana cewa akasarin mutanen da mayakan Boko Haram suka kashe Musulmi ne, yana mai cewa burin ’ya’yan kungiyar shi ne su yi amfani da addini wajen raba kan ’yan Najeriya.

A wata makala da BBC ta kalato daga daga jaridar Christianity Today, Shugaba Buhari ya ce bai kamata a kyale mayakan Boko Haram su raba kan ’yan Najeriya ba.

“A hakikanin gaskiya, kashi 90 cikin 100 na mutanen da rikicin Boko Haram ya shafa Musulmi ne: cikinsu har da ’yan makaranta mata Musulmi 100 wadanda aka sace tare da takwararsu Kirista guda daya, da kai hare-hare a masallatai da kuma kashe fitattun malaman addinin Musulunci.

“Wadannan ’yan ta’adda suna so su gina katangar da za ta raba tsakaninmu. Sun gaza a yunkurinsu na hare-haren ta’addanci, don haka yanzu suna so su raba kanmu ta hanyar sanya mu rika sukar juna,” ya bayyana a rubutun nasa.

Shugaban ya rubuta makalar ce domin yin jaje tare da alhinin kisan da wadansu da ake zargi mayakan Boko Haram ne suka yi wa wani limamin Kirista, Rabaran Lawan Andimi bayan da suka sace shi.

An hallaka Lawan Andimi ne bayan an yi garkuwa da shi a Karamar Hukumar Michika ta Jihar Adamawa a farkon watan Janairun bana a wani hari da ’yan Boko Haram suka kai a kauyensu.

Kwanaki kadan bayan da aka yi garkuwa da shi an ga marigayin a wani faifain bidiyo da ’yan kungiyar Boko Haram suka saki, yana rokon Gwamnan Jihar Adamawa Alhaji Ahmadu Fintiri ya ceci rayuwarsa.