‘Kashi 94 na ’yan Najeriya ba su samun kula a kiwon lafiya’

Shugaban kungiyar Likitoci ta Najeriya Dokta Isahon Enabulele ya ce kashi shida kadai ne na ’yan Najeriya ke samun cikakkiyar kula da lafiyarsu a kasar nan, wanda hakan ya sanya cututtuka suka yiyawa a kasar nan.Shugaban ya fadi haka ne a garin Tambuwal lokacin da kaddamar da rabon magani da duba lafiyar jama’a a kyauta […]

‘Kashi 94 na ’yan Najeriya ba su samun kula a kiwon lafiya’
‘Kashi 94 na ’yan Najeriya ba su samun kula a kiwon lafiya’

Shugaban kungiyar Likitoci ta Najeriya Dokta Isahon Enabulele ya ce kashi shida kadai ne na ’yan Najeriya ke samun cikakkiyar kula da lafiyarsu a kasar nan, wanda hakan ya sanya cututtuka suka yi
yawa a kasar nan.
Shugaban ya fadi haka ne a garin Tambuwal lokacin da kaddamar da rabon magani da duba lafiyar jama’a a kyauta da kungiyar ke gabatarwa duk shekara a ranar Talatar da ta gabata.
Dakta Isahun ya ce wannan aiki kungiyarsu ta kirkiro shi ne don ganin nan da shekarar 2014, an samu raguwarb cututtukanm da muke fama da su, “A gaskiya muna ganin alamun nasara sosai da alama
hakarmu za ta cimma ruwa don a yanzun mu canja salo mukan je kowace jiha a kasar nan cikin wata hudu tare da tawagar kwararrun likitoci da suke duba jama’a kan cututtuka daban-daban.”
Da ya juya kan yajin aikin da likitoci suke yi, ya yi kira ga gwamnati ta zauna da kungiyar likitocin domin magance yajin aiki, ya ce sulhuntawa da fahimtar juna ne kawai za su kawo karshen wannan matsala.
Shugaban Majalisar Tarayya Alhaji Aminu Waziri ya samu wakiltar Alhaji Garba Yakasai mai ba shi shawara kan harkokin lafiya, ya gode wa kungiyar kan karamcin da ta yi masa, kuma ya yi fatan alheri ga kungiyar kan shirin da take yi na taimakon ’yan Najeriya.