Kashi 99 na ’yan mata masu aure a Kano na son komawa makaranta — Bincike

An yi watsi da ra’ayin cewa addini ko al’ada na hana ’yan mata masu aure ci gaba da karatu.

Kashi 99 na ’yan mata masu aure a Kano na son komawa makaranta — Bincike

Daya daga cikin dakunan daukar karatu a Jami’ar Bayero da ke Kano

Wani bincike da aka gudanar a Jihar Kano ya nuna cewa kashi 99 cikin 100 na ’yan mata masu aure na son komawa makaranta, lamarin da ya sa gwamnatin jihar ta ƙaddamar da sabbin ƙa’idoji domin bai wa ’yan mata masu aure da iyaye mata matasa damar ci gaba da karatunsu.

An bayyana sakamakon binciken ne a ranar Talata yayin ƙaddamar da kwamitin da zai jagoranci komawar mata makarantu domin ci gaba da karatu a Jihar Kano, wanda Ma’aikatar Ilimi ta Kano ta shirya tare da tallafin fasaha daga ACE Charity da kuma tallafin kuɗi daga Asusun Malala.

A cewar masu shirya taron, binciken ya nuna cewa aure ba ya rage wa ’yan mata sha’awar neman ilimi, sai dai matsalolin kuɗi, kula da yara, kuɗin sufuri, nauyin ayyukan gida da kuma tsangwama daga al’umma ne ke hana su komawa makaranta.

Sabbin ƙa’idojin sun samar da tsarin da ya dogara da hujjoji domin bai wa ’yan mata masu aure da iyaye mata matasa damar komawa makaranta, ci gaba da karatu har zuwa kammala karatunsu.

Binciken ya kuma nuna cewa akwai gagarumin goyon baya daga al’umma a fannin ilimin ’yan mata, inda shugabannin gargajiya da na addini da dama suka yi watsi da ra’ayin cewa addini ko al’ada na hana ’yan mata masu aure ci gaba da karatu.

Haka kuma, binciken ya gano cewa maza da dama sun nuna aniyarsu ta tallafa wa matansu su ci gaba da karatu idan aka magance matsaloli irin na kula da yara, kuɗin karatu da kuma samar da sassaucin tsarin koyarwa.

Sabbin ƙa’idojin sun tanadi matakai da suka haɗa da samar da hanyoyin koyo masu sassauci, ƙarfafa cibiyoyin ilmantarwa, tallafin kula da yara da lafiyar ƙwaƙwalwa, horas da masu koyarwa, wayar da kan al’umma da kuma tsarin sa ido kan yawan waɗanda suka koma makaranta, masu ci gaba da karatu da masu kammala karatunsu.

Har ila yau, takardar ta bayyana nauyin da ya rataya a wuyan ma’aikatun gwamnati, hukumomi, makarantu, Kwamitocin Gudanar da Makarantu (SBMC), shugabannin al’umma da na addini, abokan hulɗa, ƙungiyoyin farar hula da kuma kafafen yaɗa labarai domin tabbatar da aiwatar da ƙa’idojin yadda ya kamata.

Da suke jawabi a wajen ƙaddamar da shirin, masu shirya taron sun bayyana ƙa’idojin a matsayin wani babban ci gaba a ƙoƙarin da Jihar Kano ke yi na tabbatar da cewa aure ba ya daƙile karatun ’ya mace.

Sun ce za a auna nasarar shirin ne ba wai da fitar da takardar manufofin ba, sai dai da yawan ’yan mata masu aure da iyaye mata matasa da suka samu damar komawa makaranta tare kuma suka kammala karatunsu.

Sun kuma yi kira ga abokan hulɗa, shugabannin gargajiya da na addini, iyaye, makarantu, ƙungiyoyin farar hula da kafafen yaɗa labarai da su tallafa wajen aiwatar da ƙa’idojin domin faɗaɗa damar ilimi ga ’yan mata masu aure a faɗin Jihar Kano.