Kashim Shettima ya ziyarci Kano
Wane Sarkin Kano Shettima zai kai wa gaisuwa tsakanin Muhammadu Sanusi II da Aminu Ado Bayero?
Mataimakin Shugaban Kasa Kashim Shettima ya ziyarci Jihar Kano awannin kadan bayan ya gargadi Gwamnan Jihar Sakkwato Ahmad Aliyu kan yunkurin tsige Mai Alfarma Sarkin Musulmi Muhammad Sa’ad Abubakar.
Shettima ya je Kano ne domin halartar jana’izar surukarsa, Hajiya Maryam Abubakar Albashir, wadda Allah Ya yi wa rasuwa a rabar Lahadi tana da shekaru 69.
Gwamna Abba Kabir Yusuf da jami’an gwamnatin Kano sun tarbi Shettima a filin jirgi na Malam Aminu Kano, inda suka jajanta masa game da rashin na mahaifiyar matarsa Nana.
Ziyarar ta Shettima na zuwa ne a yayin da ake ci gaba da dambarwar siyasa kan masarautun jihar.
- Tsige Sarkin Musulmi: Shettima ya gargadi Gwamnan Sakkwato
- Kano: ’Yan sanda sun kori ’yan tauri daga Fadar Sarki
Bisa al’ada dai, idan babban mutum ya ziyarci jiha, yakan kai wa sarki ziyarar ban-girma a fada.
Shin hakan zai yiwu a wannan karon? Wa Shettima zai ziyarta tsakanin Muhammadu Sanusi II da ke fadar Gidan Rumfa da kuma Aminu Ado Bayero da ke karamar Fadar Nassarawa?
A ranar ce kuma sabon Kwamishinan ’Yan Sanda ba jihar, Salman Dogo Garba ya fara aiki bayan ya karbi ragamar shugabanci daga Ussaini Mohammed Gumel.
Aminiya ta ruwaito cewa ’yan sanda sun kwace iko tare da fatattakar ’yan tauri da ’yan banga daga fadar Gidan Rumfa idan Sarki Muhammadu Sanusi II da gwamnatin jihar take goyon baya yake.
A Litinin din ne kuma Babbar Kotun Jihar Kano ta dage sauraron karar da gwamnatin jihar ta shigar tana neman kotun ta hana Aminu Ado Bayero da sauran sarakunan da aka rushe masarautunsu hudu daga gabatar da kansu a matsayin sarakuna.
Ana ganin Gwamnatin Tarayya na goyon bayan bangaren Sarkin Kano na 15 Aminu Ado Bayero wanda a Abba ya maye gurbinsa da Sanusi II.
A halin da ake ciki Aminu Ado Bayero na zaune a karamar fadar Nassarawa inda jami’an tsaro suke gadi.
Gwamnatin Jihar ta bayyana takaici bisa ci gaba da zamansa a fadar duk da umarnin da ta bayar na fitar da su domin rushewa da sabunta fadar.