Kashim Shettima zai jagoranci tawagar Nijeriya a taron MDD

Tinubu ba zai halarci taron ba saboda yana son mayar da hankali kan al’amuran cikin gida.

Kashim Shettima zai jagoranci tawagar Nijeriya a taron MDD

Mataimakin Shugaban Kasa, Kashim Shettima, zai jagoranci tawagar Nijeriya a taron Majalisar Dinkin Duniya karo na 79 da za a gudanar bana a birnin New York na Amurka.

Hakan na kunshe cikin wata sanarwa da Fadar Shugaban Nijeriya ta fitar a ranar Alhamis.

Sanarwar da mataimaki na musamman ga Shugaban Nijeriya a kan kafafen sada zumunta, Dada Olusegun, ya fitar ta ce Shugaba Bola Tinubu ba zai samu damar halatar taron ba.

Shugaba Bola Tinubu yana so ya zauna a gida domin ya maida hankali a kan wasu batutuwa na cikin gida da magance matsalolin da ke addabar Nijeriya.

“Don haka shugaban ya umarci Mataimakin Shugaban Ƙasa Kashim Shettima ya jagoranci tawagar Nijeriya,” in ji sanarwar.

Sanarwar ta ƙara da cewa Shugaba Tinubu, wanda ya koma kasar a ranar Lahadin da ta gabata bayan tafiyarsa zuwa kasashen China da Birtaniya, ba zai je Amurkan ba ne saboda yana son mayar da hankali kan al’amuran cikin gida da kuma magance wasu kalubalen da kasar ke fuskanta, musamman bayan mummunar ambaliyar ruwan da ta afku a baya-bayan nan a Maiduguri.

A taron Majalisar Dinkin Duniya 79, Mataimakin Shugaban Ƙasa Shettima zai gabatar da jawabin Nijeriya ga babban taron, da halartar muhimman abubuwan da za su gudana a taron, da kuma ganawa da wakilan wasu ƙasashen.

Babban Taron MDD mai taken “Kada a bar kowa a baya: Yin aiki tare don samar da zaman lafiya, dauwamammen ci gaba da mutunta bil’adama a yanzu da a gaba,” zai gudana ne daga ranar Talata 24 zuwa ranar Asabar 28 ga watan Satumban 2024.