Kaso 70 na yaran Nijeriya ba sa fahimtar abin da suke karantawa — Rahoto

Kashi 49 cikin ɗari na yaran da ke zuwa makaranta ke fahimtar abin da suka karantawa.

Kaso 70 na yaran Nijeriya ba sa fahimtar abin da suke karantawa — Rahoto

Hukumar da ke kula da tsare tsaren Ilimi da gudanarwa ta Ƙasa (NIEPA) ta bayyana damuwarta game da rahoton da ke nuna cewa kaso 70 cikin 100 na yaran Najeriya ba sa iya fahimtar abin da suke karantawa.

Haka kuma rahoton wanda aka fitar a kwanan nan ya nuna cewa yaran ba sa iya karatu da lissafi mai sauƙi.

Wannan bayanin yana cikin sakamakon binciken da Hukumar Auna Nasarar Koyo ya fitar wanda yake nuni da koma bayan da sha’anin ilimi yake ciki a ƙasar nan.

Darakta Janar na Hukumar NIEPA, Dokta David Shofoyeke ne ya bayyana hakan yayin da yake buɗe taron horarwa na kwanaki bakwai da aka shirya wa shugabannin makarantu su 60 akan tsarin gudanar da makaranta mai tasiri.

A cewar Dokta Shofoyeke shirin bunƙasa ilimin malamai yana da matuƙar amfani wajen magance rashin ingancin ilimi, lamarin da ya janyo hukumar ta shirya wannan horaswar a ɓangaren Arewa Maso Yammacin ƙasar nan.

“Halin da ilimin bai ɗaya yake ciki ya nuna cewa kaso 70 cikin 100 na yaran ƙasar nan ba sa iya fahimtar abin da suke karantawa haka kuma ba sa iya fahimtar lissafi mai sauki.”

Shugaban ya kuma lura cewa kashi 49 cikin ɗari ne kawai na yara da ke zuwa makaranta suke iya karatu da kuma fahimtar abin da suka karanta.

A ɓangaren lissafi kuma ya ce, kashi 55 cikin ɗari ne kawai ke iya lissafi mai sauƙi.