‘Kason da ake ware wa lafiya bai kai wa ga talaka’

An ware Naira biliyan 221 da miliyan 700 ga fannin kiwon lafiya a kasafin bana, kuna ganin ya isa?Abin da ake nufi da kasafin kudin kula da sassan kasa shi ne, a yi kudirin yin abu kaza da kaza. An kiyasta za a kashe Naira biliyan 221 da 700 kan kiwon lafiya amma wannan ba […]

‘Kason da ake ware wa lafiya bai kai wa ga talaka’
‘Kason da ake ware wa lafiya bai kai wa ga talaka’

An ware Naira biliyan 221 da miliyan 700 ga fannin kiwon lafiya a kasafin bana, kuna ganin ya isa?
Abin da ake nufi da kasafin kudin kula da sassan kasa shi ne, a yi kudirin yin abu kaza da kaza. An kiyasta za a kashe Naira biliyan 221 da 700 kan kiwon lafiya amma wannan ba lallai ba ne ya isa a yi duk abin da ake so game da kiwon lafiya. Muna dai iya cewa a bana an yi kaso mai tsoka don kula da al’amuran da suka addabi mutane da dadewa. Ba kamar a da ba, idan aka inganta hanyoyin da aka yi kudiri a kai na kiwon lafiya to a nan kusa za a iya samun nasara kan haka. Gaskiyar magana ita ce, don isa ba abin da zai taba isa. Kuma yanzu duk sukar da ake yi wa Shugaban kasa Muhammadu Buhari kashi biyu ne. Na farko wadanda suka yi sata, wadanda ba zai kyale su ba sai sun dawo da abin da suka dauka, ba kamar yadda suka yi zato ba, na ya zama nasu har abada. Na biyu shi ne, wadanda ke jingine da irin wadannan mutane. Su kuma nasu alkiblar zaginsa daban ne, domin dan Najeriya ba ya son abu daya, shi ne gaskiya, shi kuma Shugaban kasa Buhari ba zai taba yi maka karya ba. Abin da ya san zai yi ba zai ce maka ba zai yi ba, kuma wanda ya san zai yi ba zai ce maka  zai yi ba, saboda lura da kai ba ka son a yi haka. kalubalen da ke tattare da Shugaban kasa yanzu shi ne dawowa da akalar Najeriya zuwa ga gaskiya, saboda irin barnar da aka yi. Mu ’yan Arewa mu muka fi kin Buhari, don haka kowa ya tattaro hankalinsa don a samu a yi gyara.
kungiyar Mata Musulmi ta Najeriya (FOMWAN) na da alaka da abubuwan da suka danganci harkar mata da yara, wace hanya kuke bi don ganin kun cimma burinku na taimaka musu?
kungiyar FOMWAN tana da kudirori da yawa na taimaka wa mata da yara, saboda a duk duniya abu na farko shi ne a kare mata da yara, kamar yadda aka ce a cikin kasafin da aka yi na kasa. Mu ma muna kiyasta abin da za mu yi don taimaka wa mata da yara. Da yake kuma mu kungiya ce, karfinmu ba ya kaiwa mu yi duk yadda muke so, wasu lokuta mukan yi kira ga gwamnati idan abu ya fi karfinmu, kuma alhamdulillahi a duk lokacin da muka yi haka akan amsa kiranmu mu samu tallafi, mu cimma wadanda ke da bukatu.
Kun fi kusanci da mata wadanne koke-koke suke kawo muku game da lafiyarsu?
Gaskiya, maganar kiwon lafiyar nan ya na da mahimmanci, gwamnati tana iya kacin kokarinta, amma akwai neman karin su bi diddigi don su san abubuwan da ke faruwa a sauran sassan ta, domin irin kason da ake ware wa kiwon lafiya ba kadan ba ne, amma matsalar ita ce, idan kika tafi asibitin kudi, komai na kudi dari bisa dari ne, abin mamaki a nan shi ne asibitin gwamnati da aka ce an bude don a tallafa wa mutane, ya zamo yanzu ba ya da bambanci da na masu zaman kansu. Yawancin mata sukan kawo mana koke-koken rashin iya biyan kudin jinya, shi ya sa mafi yawa sukan yi zamansu a gida har su tagayyara. Don haka muna rokon gwamnati ta canja wadannan abubuwa don agaza wa marasa karfi, a bi har karkara. Saboda mata na kukan cewa wadannan kudi da ake warewa, me ake yi da su.
An sha samun kalubale kan rigakafi musamman a Arewa, me za ki ce don wayar da kan mata su yi na’am da wannan tsari?
Kin san abin da ya sa ake samun koma-baya wurin yarda da wannan tsari shi ne da Turawa suka shigo ta wajen teku suka fara bullowa kafin suka zo Arewa. Amma duk da haka FOMWAN ba mu yi sanyi wurin wayar da kan mutanenmu ba, kungiyarmu ta wanzu a ko’ina daga nan Abuja zuwa jihohi da kananan hukumomi, har da kananan kauyuka. Wannan ne dalilin da ya sa FOMWAN ke saurin cimma mutane, muna nan muna tara mata kungiya-kungiya, muna wayar musu da kai kan rigakafi, kada su dauka wayo ake yi musu, a kawo musu wani abu daban da ya saba wa addini, a’a saboda a kawar da cutar shan’inna da bakon daura ne, kuma alhamdulillahi muna samu karbuwa sosai.
A bara rahoto ya nuna cewa ba a samu bullar cutar shan’inna a daukacin Najeriya ba, wace gudumawa FOMWAN ta bayar kan wannan nasara?
Munyi aiki sosai, mun shiga kauyuka, saboda Hukumar Kula da Lafiya daga Tushe (NPHCDA) ta nemi mu yi haka. Mun yi da jikinmu da aljihunmu, ko gwamnati ta san irin dawainiyar da kungiyar Mata Musulmi ta FOMWAN ta yi.
Yaya kuke aiki da gwamnati don ku kare hakkin mata da yara?
Mukan ba gwamnati shawarwari da kuma mika rahoton duk aikin da muka yi duk shekara, mukan jawo hankalin mutane kan duk wani tsari da gwamnati ta yi wanda ya shafi inganta rayuwar mata da yara.
Bugu da kari, muna tsare-tsare da yawa da muke yi, domin mata su rika taimaka wa kansu da kansu ba tare da suna dogaro da wasu ba. Muna kuma rokon gwamnati game da kiwon lafiya ta tabbatar duk maganin da ke shigowa kasar nan sahihi ne.