KASROMA ta koka game da lalata fitilun kan titunan Katsina
Babban Manajan Hukumar Kula da Manyan Hanyoyin Jihar Katsina (KASROMA) Injiniya Jamilu Umar Hassan ya koka kan yadda jama’a ke barnata kayan wutar fitilun kan titunan jihar da aka kashe fiye da Naira miliyan 130 wajen sanya su.Injiniya Jamilu Umar ya shaida wa Aminiya haka ne a ofishinsa bayan da wata tawaga daga karamar Hukumar […]

Babban Manajan Hukumar Kula da Manyan Hanyoyin Jihar Katsina (KASROMA) Injiniya Jamilu Umar Hassan ya koka kan yadda jama’a ke barnata kayan wutar fitilun kan titunan jihar da aka kashe fiye da Naira miliyan 130 wajen sanya su.
Injiniya Jamilu Umar ya shaida wa Aminiya haka ne a ofishinsa bayan da wata tawaga daga karamar Hukumar Jibiya a karkashin jagorancin Shugaban Kwamitin Riko na karamar hukumar Alhaji Aminu Lawal suka mika masa takardar koke kan hanyarsu.
Injiniya Jamilu ya ce, makasudin kafa hukumar da gwamnatin Barista Ibrahim Shema ta yi shi ne ta gyara hanyoyi da gina sababbi tare da sanya fitilu masu bayar da hannu a hanyoyi da shatalai-talai da kuma fitilun kan tituna.
“Sai dai abin bakin ciki shi ne, duk wadannan abubuwa da ake kashe makudan kudi a kansu ana samun batagari suna lalata su ko su sace kayan baki daya. Misali shi ne, yadda aka sace wayoyin fitilun kan titin da suka taso daga Jami’ar Umaru Musa zuwa kofar kwaya da wadanda suka taso daga dandagoro zuwa kofar kaura da kuma na Barikin Soja zuwa kofar Guga da kudinsu suka kai miliyoyin Naira. Haka lamarin yake a yankin Daura da Funtuwa,” inji shi.
Babban Manajan ya ce, sun yi kokarin sanya kananan fitilun da za su rika nuna wa masu ababen hawa cewa suna kusa da gari don rage gudu.
Tun farko Alhaji Aminu Lawal ya ce, sun je hukumar ne domin mika kokensu na a gyara hanyar da ta taso daga Gurbi zuwa garin Shimfida wadda ta shafi wasu kauyuka 12, inda ya ce, aikin ya fi karfin karamar hukumar saboda akwai gadoji biyu da za a gina.
Ya bayyana muhimmanci samar da hanyar da ke da iyaka da Jihar Zamfara da cewa za ta taimaka wajen inganta tsaro da kasuwanci da noma tare da bunkasa ilimi.