Kasuwanci kwari: Yadda kyankyaso ya hada kan miliyoyin ’yan China
A duk inda aka samu lunguna masu duhu za a iya samun miliyoyin kyankyasai suna yawo musamman a jikin wadiro don neman ragowar abinci da aka rage, za a iya samunsu a wuraren zubar da shara da sauransu. Akwai yanayin da irin wadannan kwarin suke bukata kamar lokacin zafi da wuraren damshi, hakan zai iya sanya […]
A duk inda aka samu lunguna masu duhu za a iya samun miliyoyin kyankyasai suna yawo musamman a jikin wadiro don neman ragowar abinci da aka rage, za a iya samunsu a wuraren zubar da shara da sauransu.
Akwai yanayin da irin wadannan kwarin suke bukata kamar lokacin zafi da wuraren damshi, hakan zai iya sanya wadannan kwari cikin koshin lafiya.
A yayin da biranen kasar China suke ci gaba da watsar da lalataccen abinci fiye da wanda ake amfani da shi kyankyasan kasar na ci gaba da samun gindin zama a wuraren zubar da gurbataccen abincin don su kuma su samu abincin da za su rayu. A yayin da kyanyasan suka mutu wadansu sun ce, idan aka ci yana maganin ciwon ciki da maganin kyan jiki.
A wajen garin Jinan babban birnin Lardin Shandong, akwai biliyoyin kyankyasai da suke rayuwa da gurbataccen abinci da a duk rana suna cinye tan 50, wanda idan aka auna yana kaiwa nauyin matasan giwaye bakwai
Ana zubar da sharar abincin ce kafin wayewar gari kamar yadda kamfanin Shandong Kiaobin Agricultural Technology Co ya sanar. Bayan zubar da sharar abincin kyankyasan na cin abinci ta hanyar bututu.
Kamfanin Shandong Kiaobin ya ce, suna shirin kaddamar da cibiyoyi uku na dakin zubar da gurbataccen abinci a garin Jinan, wanda jama’ar garin suka kai miliyan bakwai.
A duk kasar an dakatar da amfani da gurbataccen abinci tun lokacin da aladu ke yawon cin abinci da aka zubar. Yayin da hakan yana dakile bunkasar kamfanin kyankyaso.
Shugaban Kungiyar Kamfanin Kwari ‘Shandong Insect Industry Association’ Liu Yusheng, ya ce kyankyasai wasu halittu ne masu fasaha a dakin girkin da ake zubar da gurbataccen abinci.
Kyankyasai suna daya daga cikin hanyoyin samar wa aladu abinci mai gina jiki da sauran dabbobi.