Kasuwancin bakin mai ya yi mini komai a rayuwa- Balali Mula

Ibrahim Ahmed wanda aka fi sani da Balali Mula ya shafe fiye da shekara 11 yana gudanar da kasuwancin bakin mai a Bauchi. Ya bayyana yadda ya fara kasuwancin bakin mai da kuma albarkar da ya samu. Aminiya: Tun yaushe ka fara kasuwanci bakin mai?Balali: Na fara kasuwancin bakin mai ne a tebur da jarin […]

Kasuwancin bakin mai ya yi mini komai a rayuwa- Balali Mula
Kasuwancin bakin mai ya yi mini komai a rayuwa- Balali Mula

Ibrahim Ahmed wanda aka fi sani da Balali Mula ya shafe fiye da shekara 11 yana gudanar da kasuwancin bakin mai a Bauchi. Ya bayyana yadda ya fara kasuwancin bakin mai da kuma albarkar da ya samu.

Aminiya: Tun yaushe ka fara kasuwanci bakin mai?
Balali: Na fara kasuwancin bakin mai ne a tebur da jarin Naira dubu daya da dari uku kimanin shekara 11 ke nan, wato bayan na kammala makarantar sakandare, na fara kasuwancin ne don in samu kudin da zan ci gaba da biyan kudin makaranta. Yanzu ina da manyan shaguna uku, da kuma yara kimanin 60.
Aminiya: Alherin da ka samu ta dalilin kasuwancin bakin mai?
Balali: Na gina gida, ina daukar nauyin jama’a da yawa. Ina da manyan shaguna uku. Kasuwancin bakin mai ya yi mini komai a rayuwa.
Aminiya: Matsalolin da ka fuskanta yayin kasuwancin bakin mai?
Balali: Daga farko na fara sayar da bakin mai a tebur ne, a lokacin ba ni da jari, haka na rika faduwa da tashi har Allah Ya sa komai ya daidaita.
Aminiya: Yaya kake ji idan ka ga matasa suna zaman kashe wando?
Balali: Nakan ji takaici idan na ga matashi yana zaman kashe wando domin akwai kananan sana’o’i wadanda mutum zai iya dogaro da su ba sai ya dogara da aikin gwamnati ba. Lokacin da na fara sayar da bakin mai akwai wadanda suke kallona suna min dariya, ga shi yanzu da na yi hakuri komai ya wuce. Ya kamata matasa su fara kasuwanci idan ka duba abubuwan da ke faruwa na tashe-tashen hankula a Arewa maso Gabas, to tushen matsalar daga rashin aikin yi ne, akwai da yawa daga cikin matasa da suka kammala karatunsu amma suna zaman kashe wando. Kuma idan ka duba kashi 85 cikin 100 na masana’antun wannan yanki na Arewa sun mutu, talauci ya yi yawa a Arewa, hanyar magance wannan matsala ita ce kowa ya gyara tsakaninsa da Allah.
Aminiya: Ko kana da wani kira da kake so ka yi wa gwamnati?
Balali: Ina mika kokon barata ga gwamnati da ta ci gaba da samar wa matasa hanyoyin da za su rika dogaro da kansu, akwai matasa da dama wadanda na yaye su a wannan cibiya ta inganci, kuma suna ci gaba da tallafa wa iyayensu.
Aminiya: Daga cikin matasan da suke aiki a wannan cibiya akwai masu zuwa makaranta?
Balali: Dukkan matasan da suke aiki a Cibiyar Inganci babu wanda ba ya zuwa makaranta, don haka muka raba musu aikin zuwa kashi uku akwai masu zuwa da safe, akwai masu zuwa da yamma da kuma masu zuwa da maraice, muna rufe wannan cibiya ne da misalin karfe 10 na dare. Ya kamata ’yan siyasa su daina raba kudi ga matasa, kamata ya yi su rika daukar nauyin yadda za a koya wa matasa kananan sana’o’i, a koya musu yadda ake kama kifi, ba wai a rika ba su kifin ba, wannan ita ce magana ta gaskiya.