Kasuwancin goro na raguwa sosai – Mu’azu Maigoro

Ma’azu Maigoro dattijo ne da ke kasuwancin gora a bakin Kasuwar Checheniya da ke cikin Kaduna da ya fara kasuwancin goro tun yana da shekara sha hudu da haihuwa. Me za ka ce game da kasuwancin goro? Ni kuwa ke da abin cewa game da kauswancin goro domin tun ina dan shekara 14 nake wannan […]

Kasuwancin goro na raguwa sosai – Mu’azu Maigoro

Ma’azu Maigoro dattijo ne da ke kasuwancin gora a bakin Kasuwar Checheniya da ke cikin Kaduna da ya fara kasuwancin goro tun yana da shekara sha hudu da haihuwa.

Me za ka ce game da kasuwancin goro?

Ni kuwa ke da abin cewa game da kauswancin goro domin tun ina dan shekara 14 nake wannan harka Tun ana mulkin Abba Kyari kuma har ya zuwa yanzu. Tun muna sayan bagi wato buhun goro ke nan Naira 70 zuwa Naira 80. Yanzu har Naira dubu dari biyu da saba’in muke saya.

Abin da ya sa ka gammu nan kashi- kasha, hakan ya faru ne saboda gobarar da aka yi a wannan kasuwar a shekarun baya. Sai ka ga mutum biyu can ko daya can a gefen kasuwa saboda ba mu da wadataccen waje.

A shekarun baya a kan kawo goro roka roka amma a yanzu abin ba haka ba. Ko me ya jawo hakan?

Gaskiya zamani ne ya canza domin ko a yadda masu goron ke shigo da shi a shekarun baya abin ya canza. kuma a yanzu masu cin goran ma sun ragu. Sannan kuma game da daurin aure da suna mafi yawanci yanzu mutane sun koma masallaci ba a taruwa a kofar gida kamar yadda ake yi a da.

Ka ga bambancin ke nan yanzu da kuma a da. Kuma ni a tunanina talauci ne ya kawo haka. Duk mutumin da ka ga ya samu arzikin daurin aure ko rada suna bai tara mutane a kofar gidansa an yi bayani ba bai samu yadda yake so ba. Hakan na nuna akwai talauci.

A da roka nawa kake saukewa na goro?

Ni din nan a shekarun baya a duk watan duniya roka guda ake kawo min na goro. Amma a yanzu huhu hamsim ma sai ka kwashe kwan ashirin da hudu bai kare ba. Amma ko a da sai an kawo min roka guda na goro kuma su kare cikin lokaci.

A wane zamani ke nan kake wannan maganar?

A zamanin mulkin Shugaban Kasa Shagari ne. Amma a yanzu sai a kawo mana huhu hamsin ma kadai amma bai kare ba a wata.

Daga ina ake kawo muku goran a wancan lokaci?

Ana kawo mana daga Shagamu da Agege da Ile-Ife da kuma wanda ake kawo mana daga kasar Ghana.

Yanzu ko akwai wani kasuwa na ’yan goro a Jihar Kaduna?

Babu wani kasuwa da za a ce na ’yan goro ne a nan Kaduna a yanzu, amma a da akwai. Da akwai a nan Kasuwar Shaikh Gumi sai kuma Bakin Gate. Amma yanzu sai nan bakin dogo a yanzu kuma ko a can din ma sai dai ka ga mata can biyu, can uku. Duk an koma a warwatse.

Su masu zuwa saye don ci sun daina ko suna zuwa?

Suna zuwa saye sai dai ba kamar da ba. Masu sha’anin ma sanda Allah Ya kawo, wani na zuwa ya saya huhu daya wani biyu wani goma, haka dai-dai suke zuwa daidai karfin mutum. Amma fa cikin kashi dari na masu zuwa sayen goro, kashi chasa’in ya ragu.