‘Kasuwancin kubewa akwai riba sosai’

danliti Abdulrahman babban dillalin kubewa a Gadabi zuwa Sabon Gari da ke karamar Hukumar Kwali a Abuja ne, yana sayar da kubewa sassan kasar nan ciki har da yankin jihohin Igbo. A hirarsa da Aminiya ya bayyana ribar da ake samu wajen kasuwancin kubewa, da kuma kalubalen da yake fuskanta a lokacin damina. Ga yadda […]

‘Kasuwancin kubewa akwai riba sosai’

danliti Abdulrahman babban dillalin kubewa a Gadabi zuwa Sabon Gari da ke karamar Hukumar Kwali a Abuja ne, yana sayar da kubewa sassan kasar nan ciki har da yankin jihohin Igbo. A hirarsa da Aminiya ya bayyana ribar da ake samu wajen kasuwancin kubewa, da kuma kalubalen da yake fuskanta a lokacin damina. Ga yadda tattaunawar ta kasance:

Aminiya: Yaya kake gudanar da kasuwancin kubewa?

danliti: Nakan sayi kubewa mai yawa a wurin Fulani, sai in dure a buhuna sannan in sayar sassan kasar nan. Na shafe shekara 17 ina wannan sana’ar, a yanzu haka ina da gonar kubewa a Gadabi.
Aminiya: Za a iya cewa don ba ka iya noma abin da kake bukata ne ya sanya kake sayan kubewa a wurin Fulani?
danliti: Ban cika noman kubewa kowane lokaci ba, hakan ya sanya nake saye daga wurinsu. Kasancewar ni babban dillali ne, kuma ina bukatar kubewa mai yawa, don haka gonata kawai ba za ta iya samar da kubewar da nake bukata ba.
Aminiya: A ina ka fi sayar da kubewarka?
danliti: Nakan sayar wa kwastomina a Jihar Imo da Enugu da kuma Abiya. Idan na tura buhunan kubewa yau, gobe za a sa sayar da su. Saboda idan ta dade to za ta lalace. Nakan bi wadanda na tura don in duba yadda ake sayarwa, na fahimci an fi samun riba idan ina nan.
Aminiya: Ba ka sayarwa a Abuje ne?
danliti: Ba na sayarwa a Abuja saboda ana noman kubewa sosai a nan. Za ka samu kubewa a ko’ina a nan, don haka babu riba sosai.
Aminiya: Naira nawa kake sayan kwando a wurin Fulani?
danliti: Idan lokacin rani ne, nakan sayi kowane kwando Naira 2, 500. Amma idan lokacin damina nakan sayi kwando a kan Naira 300 zuwa 500, dalili kuwa shi ne, kwastomomi ba su cika sayen kubewa lokacin damina ba, hakan ya sanya take araha.
Aminiya: Naira nawa kake sayar da buhun kubewa a lokacin damina?
danliti: Babu wani kayyadadden farashi a lokacin damina. Wani lokaci nakan sayar da buhun kubewa a kan Naira 1, 000 ko Naira 700, wani lokaci har kasa da haka. Amma a lokacin rani tsada take yi.
Aminiya: Wadanne nasarori ka cimma dalilin kasuwancin kubewa?
danliti: Na auri mata biyu, ina da ’ya’ya 4, kuma ina daukar nauyinsu daidai gwargwado. Matana babu wacce take aiki, suna gida suna lura mini da ’ya’yana. Na mallaki gida da babur wanda nake amfani da shi zuwa kauyuka.
Aminiya: Wadanne kalubale kake fuskanta a wannan harkar?
danliti: Babban kalubalen da nake fuskanta shi ne samun yin zarafin jigilar kubewar da nake sayarwa ba tare da matsaloli ba. Misali idan zan kai kayana Jihar Imo, a da nakan biya Naira 4, 000, amma a yanzu nakan biya Naira 16, 000, saboda gwamnati ta kara kudin-shigar da ake karba a kan hanya. Ina fata gwamnati za ta sassauta mana.